HAKKOKI A MUSULUNCI

HAKKOKI A MUSULUNCI

HAKKOKI A MUSULUNCI

(0 Votes)

QRCode

(0 Votes)

HAKKOKI A MUSULUNCI

Muna godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan Littafi game da hakkokin zamantakewar al'umma. Wannan littafin an wallafa shi ne da nufin isar da sakon gyara da sanin ya kamata tsakanin juna a zamantakewa a matsayin al'umma daya, da kuma sanin hakkin Allah (S.W.T) da na mutum a kan dan'uwansa mutum da kokarin ganin kiyaye hakan. Sanin hakkokin Allah da halittarsa da suke kanmu wani abu ne wanda yake mafi muhimmanci a rayuwarmu, domin da shi ne zamu iya tasra rayuwarmu ta duniya da lahira. Tun asali ma ba komai ne kasancewar al'umma mai kamala da sanin ya kamata ba sai kasancewarta ma'abociyar kiyaye dokoki da hakkokin da yake kanta na mahaliccinta da na sauran halittu da suka hada da mutane da dabbobi da sauran samammu, wannan kuwa a matsayinta na daidaiku ne ko a matsayinta na jama'a. Mun yi amfani da misalai masu yawa a littafin domin ya zama kusa da cimma abin da muke so na fahimtarsa, don cimma buri na kawo gyara ga al'umma da yanayin da kowa zai iya karantawa ya kuma fahimci sakon da ake son isarwa. Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga Ahlul Bait (A.S) kuma ya karbi wannan dan kokari namu ya taimake mu a kan hidimar addininsa.

Hafiz Muhammad Sa'id

Related Titles