Drawer trigger

TARIHIN SHI'A DA AKIDOJIN TA

TARIHIN SHI'A DA AKIDOJIN TA

TARIHIN SHI'A DA AKIDOJIN TA

Publication year :

2005

(0 Votes)

QRCode

(0 Votes)

TARIHIN SHI'A DA AKIDOJIN TA

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukaki. Tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakon Annabawa da Manzanni, Muhammadu dan Abdullahi (SAWA), wanda Allah Ya aiko a matsayin rahama ga duniya baki daya; da tsarkakan iyalansa, wadanda Allah Ya kawar da duk wata dauda daga gare su Ya kuma tsarkake su ta ko’ina; da zababbun Sahabbansa daga Muhajirun da Ansar, wadanda suka yi imani da shi, suka yi jihadi tare da shi, suka taimake shi kuma suka kafu a kan shiriyar da ya bari bayansa; da sauran Muminai maza da mata masu bin shiriyar wadancan zababbu. Bayan haka. Tun kimanin shekaru goma sha hudu da suka wuce na rubuta littafin Tarihin Shi’a da Akidojinta, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan mutane game da ainihin tarihin Shi’a da irin akidun dake tattare da ita. A wancan lokacin, manufata ta kasance kalubalantar irin katobara da wasu marubuta da masu wa’azi ke yi, a kokarinsu na yiwa mutanensu bayani a kan ’yan Shi’a da akidunsu. Mafi yawan abubuwan da wadancan suka rika fada a lokacin, kuma suka ci gaba da fada har zuwa yau kurakurai ne; a inda kuma suka fadi gaskiya sai sun hada da magudi, da cin amanar ilimi da gabatar da ra’ayoyi. Littafin ya amsa bukatar wallafa shi din. Domin daga wasiku da zantuka da mutane dabam daban suka yi ta yi da ni, na fahimci irin tasirin da ya samu wajen rage irin wadancan kage-kage da kurakurai a kan Shi’a. Har ila yau littafin ya yi wani aiki da ban yi tsammaninsa ba a da can, shi ne ya taimaka wajen karfafa mutane wajen komawa da yin bincike a kan Shi’a, daga karshe dubbai sun haskaka da samun baiwar shiga sahun mabiya ’ya’yan Ma’aiki (SAWA). Duk da haka, daga baya na fahimci gazawa da kurakuraina a nan da can. Wasu daga bangaren ’yan’uwa da suka karanta littafin karatun neman kuskure kuma suka same su tare da wadanda a hanyar karatun da suka yi ne na neman karuwa suka gano wadancan kurakurai; duk bangarorin sai suka tsinkayar da akan haka, nan take na kuduri aniyar cewa duk rananr da Allah Ya ba ni ikon sake buga shi zan yi iyaka kokarina wajen kiyayewa. Na godewa kowa a kan haka, kuma ina fatan Allah Ya saka musu da alheri. A ’yan shekarun baya bayan nan ne mutane da dama suka ji bukatar sake buga wannan littafi. An tuntube ni a kan haka a lokuta da wurare dabam daban; jinkirin da na yi har ya sa wasu suka yi niyyar bugawa da kansu, amma na yi ta ba su hakuri saboda wani sabon shiri da nake da shi; wannan kuwa shi ne kara fadada shi don ya dace da yanayin da ake ciki yanzu, ya kuma amsa bukatun yau, wadanda sun ketare na sama da shekaru goma da suka shude. Don haka sai na aiwatar da hakan. A yayin kwaskwarimar da na yi, na yi kokarin fadada bangaren tarihin shugabannin Shi’a, wato Ma’asuman al’ummar nan goma sha hudu: Annabi Muhammadu (SAWA), da Sayyida Fadima al-Zahra (AS) da Imaman al’umma goma sha biyu, farawa da Imam Ali bin Abi Dalib (AS) har zuwa na karshen su Sahibuz-Zaman, Imam al-Mahdi al-Muntazar (AF). Dalilin fadada wannan bangare shi ne fahimtar da na yi na bukatar samun masaniyar da ta wuce wadda ake da ita a halin yanzu a kan su. A karshe sai a fagen Akidun Shi’a, wanda nan ma na fadada bangaren Usuluddin, da suka taro imanin mu kan Tauhidi, da Annabci, da Imamanci da Makoma. Haka na kara bayanin wasu akidun, don fahimtar da na yi na bukatar sanin makamar Shi’a da matsayinsu a kansu. Wannan ya sa dole yanzu littafin ya dauki sabon salo don cimma wannan manufa. Sabon salon kuwa shi ne kasa littafin zuwa juz’o’i biyu.  Kowane juz’i kuma ya kunshi sassa biyu. Juz’in farko, wanda shi ne wannan da ke hannun mai karatu, yana da sassa biyu. Sashin farko zai yi nazari ne a kan tarihin kafuwar Shi’a, wato lokaci da wanda ya kafa asasin farko na ginin ta. Hakan zai zo ta hanyar shiga tarihi da jin abin da galibin wadanda suka yi magana a wannan fanni suka fada, da nazarin zantukan kowa da ma’aunin shari’a da hankali. Akwai kwatanta zantukan da fitar da gaskiya ta wani bangare; da karya, da kuskure da/ko kage, ta wani bangaren. Daga nan kuma sai sashi na biyu, a wannan juz’in dai, wanda ya fara kawo tarihin Ma’asuman al’umma goma sha hudu. Farawa da Manzon Allah (SAWA) har zuwa Imami na biyar daga jerin Imamai goma sha biyu, wato Imam al-Bakir (AS). Karshen tarihinsa ne karshen wannan juz’in; saura kuma yana farkon juz’i na biyu. Wannan ne zai saukaka zarafi da dawainiyar bugun littafin,  da kuma gujewa gajiyar da mai karatu abubuwa da yawa cikin littafi daya mai yawan shafuka. Na yi kokarin dangana kowace magana ga mai ita, tare da ambaton littafi: juz’i da shafin da na sami maganar. Mai son bincike na iya komawa ya duba. Sai dai bugun littafai kan bambabta a mafi yawan lokuta, don haka ba dole ne mutum ya sami a bin da na fada a juz’i ko shafin da na ambata ba; sai dai inda na ambaci babi, to nan kam ba kasafai akan sami wani bambanci ba. A daukacin littafin na bayyana fahimtata ne. Don haka na dauko zantukan wasu ne don karfafa wani matsayi nawa, ko don tabbatar da korewar wani abin. Na yi amfani da littafan Ahlussunna fiye da na Shi’a a wannan littafin a matsayin Sai Mai Shaida  Daga Mutanenta Ya yi Shaida. Wannan ya fi karfi wajen tabbatarwa da ’ya’uwa Ahlussunna madafar ’yan Shi’a daga littafansu. Abin da ya sabawa haka, a cikin littafan na su kuwa, ba mu da bukatar fitar da shi da kafa hujja da shi, don ba mu yarda da shi ba. Da wannan kamar muna cewa ne: “Mun dace da ku a nan, mun kum saba a can”. Don haka: “Ku zo mu duba inda muka dace, don ya zama asasin da za mu gina hadin-kan mu”. Daga nan   kuma sai kowa ya kebanta da abin da ya saba da dan’uwansa ba tare da wani kunci ba. Matsala na faruwa ne kawai a lokacin da wani ya ga cewa dole kowa ya yarda da abin da ya yarda da shi ko ya yi abin da yake yi; wanda wannan ba mai yiwuwa ba ne. Kamar yadda na fada tun tuni, sanin makaman juna shi ne asasin hadin-kai mai karko. Jahiltar fahimta da tunanin juna na iya haifar da mummunar gaba ga ’yan gida daya ma balle wasun su. Tare da fatan amfana da addu’a, nake gabatar da Juz’i na farko na littafin Tarihin Shi’a da Akidojinta zuwa ga mai karatu. Ba zan bar wannan dama ta wuce ba har sai na mika godiya ta masamman ga wasu bayin Allah, wadanda ba don su ba da wannan aiki ba shi da hanyar bayyana; wadanda ba don irin kyakkyawar niyyarsu ta hana ambaton sunayensu ba da na kasafto su a nan don mai karatu ya kara mika godiya gare su. Amma duk da haka, sai na yi karambanin ambaton mutane irin su Salisu Alhassan (Babban Jihadi), da Alhaji Abdulhamid Barambu (dukkan su a Gombe), wadanda su ne jigogin sake bugun littafin a mataki na biyu; a tare da su akwai wadanda suka taimaka da lokuta da shawarwari da sauran hanyoyin tagazawa, irin ’yan kungiyar Ahlul-Baiti Muslim Community ta jihar Gombe, ina gode musu kan irin goyon bayan da suka yi ta ba ni, ba kawai kan wannan aiki ba, a fagage masu yawa. Ina rokon Allah Ya gode musu, haka ma ManzonSa (SAWA) da Ahlulbaiti (AS). Ina rokon mai karatun da ya amfana da wani abu daga littafin da ya yi musu addu’ar kariya daga Allah, da karin budi da taimakonSa a ko’ina suke. Haka ina godewa abokan aikina Sheikh Muhammad Nuru Das da Sheik Bashir Lawal, wadanda suke ba ni goyon baya a kan irin wadannan ayyuka da fagage dabam daban da suka shafi bunkasa da ci-gabana, kuma suka taimaka wajen ganin bugu na uku ya tabbata. Lallai ba don hadin kansu da kyakkyawan zatonsu ba da bugu na uku, in har ya yiwu, ya tsawaita. Allah Ya saka musu da alheri Ya kuma kara musu haske a duk bangarorin rayuwarsu. Haka ta bangaren Iyali, dole na jinjinawa matata da tarihin buga littafin ke damfare da ita. Ba shakka ta dauki hakurin yankewa daga mijinta da rashin samun hankalinsa na lokuta masu yawa a tsawon shekarun da aka yi ta buga wannan littafi. Na gode mata da hakurinta da fahimtar da ta nuna, Allah Ya bar mu tare, kuma Allah Ya saka mata da mafi alherin sakawa. Haka duk sauran Iyali na daga iyaye da ’yan’uwa, wadanda keda hakkin zumunci kuma sadar da wannan hakki ya sami tangarda saboda wannan aiki. Allah Ya huci zuciyarsu Ya kuma saka musu da alheri. Ga kowa da kowa da wannan aiki ya shafa, daga bugunsa na farko har zuwa wannan, na ke cewa: Na gode Allah Ya saka muku da alheri. Kuma Allah Ya ji-kan Iyaye da kakanni da dangi da abokan arziki. Allah ni ke roko da Ya sanya duk wata fa’ida da aka samu a wannan littafi ta zama makankara ga duk abin da na gaza a cikinsa da zunubbaina baki daya. Allah Ya sa ya zama matsera gare ni, saboda ba ni da wani tanaji na kashin kaina da zan iya daga kai in dubi mutane da shi a gobe lahira. Hakika kuwa Allah mai tausayi ne mai amsa addu’a. Walhamdu lillahi Rabbil’Alamin.   Saleh Muhammad Sani Zaria E-mail: [email protected] 26 ga Safar, 1426 Hijriyya. 5 ga Afrilu, 2005 Miladiyya.