Mukamin Ahlul baiti (A.S)
Mukamin Ahlul baiti (A.S)
Sect :
shia
Translated :
اصلی
Source :
personal archive
0 Vote
76 View
Ahlulbaiti (A.S) suna ne mai haskakawa, kuma daukaka ce madawwamiya, sannan suna ne da yake abin kauna ne ga duk rai mai kaunar Manzon Allah (S.A.W) kuma ya yi imani da shi, kuma yake rayuwa bisa shiriyarsa (S.A.W). Hakika musulmi sun san wannan madaukakin suna cikin tarihi da kuma cikin martabar nan da take rataye da Alkur'ani mai girma, tun lokacin da Alkur'anin ya yi furuci da wannan sunan mai albarka, kuma ya sanyawa wannan tauraruwan (Ahlulbaiti) lakabin da babu irinsa a duniyar dan Adam: "....Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" (Surar Ahzab, 33:33) Da saukar wannan aya mai albarka wani tafarki ya ayyana a matsayin wani abin dogaro da mafuskanta a rayuwar Musulunci. Alkur'ani ya juya fuskoki zuwa ga wannan tafarki tare da tabbatar da dukkan haske a bisa wannan a kan gaba wajen jagoranci. Har ila yau ya bayyana rawar da Ahlulbaiti (a.s) za su taka a rayuwar al'ummar musulmi, ya kuma kebance su da nufin tsarkakewa, abin karfafawa daga Gwani, Masani. Lalle wannan aukuwa mai girma tana da wata kebantacciyar ma'ana a rayuwar al'umma da gina tarihinta da wayewarta. Wannan ma'ana kuwa dukkan masu bincike da tahkikin Musulunci da kuma fagen rayuwar siyasar wannan al'umma sun san da ita. Hakika wadannan ayoyin sun ayyana wata cibiyar harkar tarihi bayan Manzon Allah (S.A.W), harkar da ta dace da al'ada da tsarin hujjar da Musulunci ke dogara da shi. Wannan ya biyo bayan baiwar da Allah Ya yi wa tatattun nan masu albarka (Ahlulbaiti), baiwa ta tsarka-kewa daga zunubai da sabo da kuma laifi. Hakika Alkur'ani mai girma ya tabbatar musu da mafificiyar darajar falala da kuma mafi girman martabobin cancanta, da'a da shugabanci a rayuwa ta Musulunci wacce falsafarta a rayuwa ita ce: "Lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa". (Surar Hujurat, 349:13 Babu shakka duk wanda ya bibiyi Alkur'ani mai girma da sunnar Annabi (S.A.W) tsarkakkiya zai samu cewa mutanen gidan Annabi mai daraja (S.A.W) suna da matsayi kebantacce da muhalli mabayyani. Za a ga cewa shugabannin wannan al'umma da malamanta da masu fassara da masu ruwaya da ma'abuta tarihi da malaman fikihu da masu yawan ibada duk suna ba da labarin wannan matsayi na Ahlulbaiti (a.s) ta dukkan fuskoki da hanyoyi. Lallai littattafan hadisi, tarihi, tafsiri da na adabi da wake da darajoji wadanda musulmi daga mazhabobi da hanyoyin ilmi daban-daban suka wallafa, sun bayyana kebantaccen matsayin da muhalli muhimmi na Ahlulbaiti (a.s). Wadannan littattafai suna magana a kan daukakar wannan itaciya mai albarka. Ana auna imanin mumini ne da kaunar Annabi (S.A.W) da Ahlubaitinsa da rige-rigen sanar da al'umma darajojin Alayen Manzo masu daraja da nutsar da kaunarsu cikin rayuka, da bayyana gajin hakuri da jin ciwon halayyar wadanda suka yi gaba da mutanen gidan Annabi mai daraja, kuma suka cutar da su da ababen kunya da kuma bala'u. Lallai mutanen wannan gida tamkar tauraruwa ce wacce babu kamarta, domin ilmin da suke dauke da shi da kuma takawa da halayen kwarai da darajoji madau-kaka da kare Musulunci da ilminsu da kuma daukar takobi da yaki da zalunci da keta haddi. Domin haka ne musulmi suka dace a kan cewa babu wani daga cikin wannan al'ummar da ya mallaki mukami da daukaka da daraja irin wanda Allah Ya kebance Ahlulbaiti da su…su kadai Allah Ya kebance da tsarkakewa daga dauda da zunubi: "...Allah na nufin Ya tafiyar da kazamta kawai daga gare ku, Ya ku mutanen babban gida, kuma ya tsarkakeku tsarkakewa" Kuma su kadai ne Allah Ya kebance da wajabta kaunarsu a kan wannan al'ummar Ya kuma sanya kaunar ta su wani hakki na Annabi (S.A.W) a kan al'umma: Ka ce: "Ban tambayar ku wata lada a kansa, face dai soyayya ga makusanta....". (Surar Shura, 42:23) Kuma su kadai ne Allah Madaukakin Sarki Ya wajabta yi musu salati a cikin salloli biyar, Yana gwama ambatonsu da ambaton ManzonSa (S.A.W): "Lalle Allah da Mala'ikunSa suna yin salati wa Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi". (Surar Ahzab, 33:56). Manzon Allah (S.A.W) ya riga ya koyawa al'um-marsa yadda za ta yi salati a gare shi da alayensa yayin da suka tambaye shi: Ya ya za mu yi salati a gare ka Ya Rasulallah? Sai ya ce da su: "Ku ce: Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu da Alayen Muhammadu kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da Alayen Ibrahim, lallai Kai ne Abin godiya, Mai girma" To babu wanda yake da wadannan darajoji da siffofi cikin wanna al'umma face su. Wannan shi ya sanar da mu daukakar Ahlulbaiti (a.s) da matsayinsu, da wajibcin kaunarsu da koyi da su da kuma tafiya bisa turbarsu. Ba don kome ne Alkur'ani ya jaddada a kan mutanen wannan gida, ya kuma bayyana matsayi da mukaminsu ba, sai domin a yi koyi da su bayan Manzon Allah (S.A.W) da kuma riko da sonsu da karbar (dukkan ilmi da shiriya) daga gare su. Babu abin da yasa Alkur'ani ya sanar mana da Ahlulbaiti (a.s) ta hanyar da ya nuna mana su face domin wasu dalilai na akida da abin da ya danganci sakon Musulunci kaco-kam, dalilan da suke sa dukkan wani musulmi ya dora tunani mai zurfi da lura da kuma kokarin riskar da kwakwalwarsa hakikanin wannan jama'a (Ahlulbaiti) da take a kan gaba wajen karbar sako. Wannan jama'a kuwa ita ce Allah Ya yi wa baiwar matsayi na shugabanci a cikin al'umma, bayan Alkur'ani da Manzo (S.A.W) sun yi masu wannan gabatarwa. A nan gaba za mu bijiro da gabatarwar da Alkur'ani mai girma da Sunna mai tsarki da shuwagabannin musulmi da malamansu da masu adabi suka yi wa wannan itaciya mai albarka, zuriyar mai tsarki, wacce ita ce madugun al'umma.