AL-BADA'U -SAMUN CANJIN RA'AYI
AL-BADA'U -SAMUN CANJIN RA'AYI
Author :
Interpreter :
(0 Votes)
(0 Votes)
AL-BADA'U -SAMUN CANJIN RA'AYI
Lallai yana daga cikin dabi’ar mutane su yi sabani a junansu, sai dai Allah yana son wannan sabanin ya takaita a cikin kewayen ingantaccen imani, saboda haka ne ba makawa ya zamanto akwai ma’auni tabbatacce da masu sabani zasu koma zuwa gare shi. Allah madaukakin sarki ya saukar da littafi da gaskiya domin ya yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya cikin abin da suka saba a cikinsa[1]. Da babu wannan gaskiya guda daya, to da al’amarin rayuwa ba zai daidaitu ba, Wannan shi ne abin da Kur’ani yake tabbatar da shi kuma yake bisa ka’idar tauhidi, sannan sai daga baya aka samu karkata da sabani da camfe-camfe har mutane suka nisanta daga wannan asasi nisanta mai girma. Ta haka ne ta bayyana cewa mutane ba su ne masu cancantar su yi hukunci da gaskiya ko karya ba matukar sun kasance suna iya biye wa son rai da bata da zalunci. Duk da littafin Allah ya sauka da shiriya ya kuma isa zuwa ga mutane…. tare da hakan son rai ya rinjayi mutane nan da can, kwadayi da tsoro da bata suka nisantar da mutane ga karbar hukuncin littafi da komawa zuwa ga gaskiya da yake dawo da su zuwa gareta. Bata shi ne ya jagoranci mutane a tsawon zamani zuwa ga sabani da shisshigi da kin Allah, Jahilci ya zama wani sababin sabani da rarraba, sai dai shi jahili ya kamata ne ya tambayi malamai kamar yadda Allah ya fada: “Ku tambayi ma’abota sani idan ba ku sani ba[2]”. Ta haka ne ketare iyakar jahili ya kasance zalunci da shisshigi ga wannan asali wanda hankali yake amincewa da shi, kuma ma’abota hankula suke karkata zuwa gareshi, kuma lallai wannan shi ne mafi bayyanar ka’idoji da hanyoyi wadanda zasu toshe hanyar rarraba da sabani. Musulunci shi ne addinin Allah dawwamamme da hakikarsa ta bayyana cikin nassin littafin Allah (S.W.T) da sunnar manzonsa (S.A.W) da ba ya magana da son rai sai da wahayi. Kuma Allah da manzonsa sun sani cewa al’ummarsa zata yi sabani bayansa kamar yadda ta yi sabani a lokacin rayuwarsa, don haka ne Kur’ani mai girma ya sanya wa al’umma makoma da zasu dogara da ita bayan wafatin manzo (S.A.W) tana tafiya tare da shi taku-taku tana kuma gabatar wa al’umma abin da suka takaita ga fahimtarsa da tafsirinsa, wannan kuwa su ne; Ahlul Baiti (A.S), sun tsarkaka ne daga dukkan dauda da kuma kazanta wadanda Kur’ani ya sauka ga kakansu Mustapha (S.A.W), suna karbarsa suna karanta shi suna hankaltarsa da kiyayewa, sai Allah ya ba su abin da bai ba waninsu ba... Kamar yadda manzo ya yi wasiyya da su a matsayin makoma ta gaba daya a hadisin sakalain mash’huri, sai suka kwadaitu wajan kare shari’ar musulunci da Kur’ani mai girma daga fahimta ta kuskure da tafsiri na barna, suka saba da bayanin ma’anarsa madaukakiya, sai suka zama makoma kuma madogara ga al’ummar musulmi, suna kore shubuha suna masu karbar tambayoyi da hakuri da juriya. Bayan nan abin da suka bari mai yawa yana shaidawa da kyawon mu’amalarsu tare da masu tambayarsu da tattaunawa da su, kuma komawa garesu da zurfin amsawarsu yana nuni zuwa ga kasancewarsu makoma ta ilimi a wannan fage. Hakika koyarwarsu ta kare abin da suka bari, kuma mabiyansu suka kwadaitu a kan kare shi daga tozarta, abin da yake nuni zuwa ga koyarwarsu da ta tattaro dukkan wasu rassa na ilimomin da suke kunshe cikin koyarwar addinin musulunci. Kuma wannan makaranta ta iya tarbiyyatar da mutane da suke shirye domin kamfata daga wannan ilmi kuma ta fitar wa al’umma manyan malamai masu biyayya ga tafarkin Ahlul baiti (A.S), suna masu gamewa da sanin dukkan mas’alolin mazhabobi daban-daban, da kuma akidoji a cikin da’irar musulunci da wajanta, suna masu bayar da mafi kyawon amsa da bayanai a tsawon zamanin da ya gabata. Hakika majma Ahlul baiti (A.S) ya gaggauta yana mai farawa daga nauyin da yake kansa da ya dauka a kafadunsa domin kariya ga sakon musulunci wanda ma’abota mazhabobi da kuma masu akidu da suka saba wa musulunci suka damfaru da su, yana mai bin tafarkin Ahlul Baiti (A.S) da mabiyansu da suka kwadaitar da raddi kan kalu-balen wannan zamani da kuma kokarin dawwama a kan tafarkin gwagwarmaya daidai gwargwadon abin da kowane zamani yake bukata. Ilimin da littattafan malamai masana ma’abota bin koyarwar Ahlul baiti (A.S) suka taskace shi a wannan al’amari ba shi da misali, domin shi madogara ce ta ilmi da yake karfafa da dogara da hankali da hujja, yake kuma nisantar son rai da zargi, yake kuma magana da malamai masu tunani daga ma’abota kwarewa, maganar da hankali yake yarda da ita kuma dabi’ar dan Adam kubutacciya take karbar ta. Kokarin majma ya zo ne domin ganin an gabatar wa dalibai sabuwar marhalar wannan ilimi mai wadata a shafin tattaunawa da tambaya da kuma raddin shubuha da a kan tayar daga lokaci zuwa lokaci tsawon zamani, ko kuma ake kawo wa a yau musamman ma da taimakon wasu kungiyoyi masu kin musulunci da musulmi a cikin sarkar sama ta intanet da makamantansu, muna masu nisantar abin da yake maras kyau, muna masu kwadayin motsa tunanin masu hankali da masu neman gaskiya domin su bude idanunsu a kan gaskiyar da koyarwar da Ahlul baiti (A.S) suka gabatar wa duniya baki daya a zamanin da hankula suke cika, alakar mutane da tunani take samuwa cikin gaggawa. Ba makawa mu yi nuni da cewa wannan tattararrun bahasosi an tanade su ne a lujna ta musamman da Hujjatul Islam Abul Fadal Islami yake shugabanta tare da wasu manya da suka hada da Sayyid Munzir Hakim, da Shaikh Abudlkarim Bahabahani, da Sayyid Abdurrahim Musawi, da Shaikh Abdul Amir Assuldani, da Shaikh Muhammadul Amini, da Shaikh Muhammad Hashimi Al’amili, da Sayyid Muhammad Rida aali Ayyub, da Shaikh Ali Baharami, da Husaini Salihi, da Aziz Al’ukabi. Kuma muna mika godiya mai yawa ga dukkan wadanan da kuma ma’abota falala da bincike da suka hada da: Shaikh Yusuf Garawi, da Shaikh Ja’afarul Hadi, da Ustaz Sa’ib Abdulhamid, domin bibiyar da kowannensu ya yi wa wadannan bahasosi da kuma bayanansu masu kima. Fatanmu shi ne ya zama mun gabatar da abin da zamu iya na kokarin sauke nauyin da yake kanmu game da wannan sako mai girma na ubangijinmu da ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya domin ya daukaka shi a kan dukkan wani addini kuma Allah ya isa shaida.