Drawer trigger

HADA SALLOLI BIYU

HADA SALLOLI BIYU

HADA SALLOLI BIYU

(0 Votes)

QRCode

(0 Votes)

HADA SALLOLI BIYU

Mazhabobin musulunci gaba daya sun hadu a kan halarcin hada sallar azahar da la’asar a lokaci guda, da kuma tsakanin sallar magariba da issha a lokaci daya, amma an yi sabani a kan dalla-dallan wannan Magana ta fuskacin sharudda da dalilan da zasu sa haka, daga ciki akwai wanda ya tafi a kan cewa ya halarta a Arfa da Muzdalifa, daga ciki akwai wanda ya kara da lokacin safara, da dai sauransu. Amma abin takaici shi ne sai ga wasu suna tuhumar makarantar Ahlul baiti (A.S) da cewa sun saba wa shari’a, saboda kawai su sun yi hukunci da cewa hada salloli biyu ba uzuri ma ya halatta, alhalin dalilin shari’a a gun jama’a biyu (Sunna da Shi’a) suna karfafa halarcin kamar yadda zamu gani. Don haka ne zamu yi bincike game da wannan mas’ala gun wadanda ba mabiya Ahlul baiti (A.S) ba, da kuma dalilan shari’a da suka dogara da ita mu ga hakikanin asalinta daga asalin shari’a, sannan sai mu yi la’akari da matsayin Ahlul baiti (A.S) kan wannan mas’ala cikin wadannan bayanai masu zuwa: