Drawer trigger

ABOTAKA

ABOTAKA
Mu'assasar Al-Balagh
Tsarawar: Hafiz Muhammad Sa'id
Kur’ani Mai Daraja:
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .
Abota Da Abokai
Tun farko-farkon yarinta, hatta ma kafin yaro ya koyi magana, yakan fara komawa da kuma kaunar yaran da suke tare da shi a cikin gida. Yakan yi wasa da rige-rige da su kan abubuwan wasa ko kuma halawa da dai sauran abubuwan da suke hannayensu... Hakika irin wannan komawa ta dabi'a zuwa ga sauran mutane da yaro yake yi, bugu da kari kan wasa da sauran yara 'yan'uwansa, yana nuni da irin sha'awar zaman tare da ke tattare da dan'Adam….. Don kuwa an halicci mutum (cikin hikimar Ubangiji) ne don ya rayu cikin al'ummar, don haka ne sha'awarsa da kuma ruhinsa da ke son rayuwa tare da sauran mutane suke tura shi zuwa ga kulla alaka tare da sauran mutane. Don haka kuma mutum yakan ji kadaitaka da kuma damuwa a duk lokacin da ya kasance shi kadai ba tare da wani a kusa da shi ba. Ba wai kawai hakan ba, lalle dan'Adam dai yana bukatuwa da waninsa kamar yadda wanin nasa shi ma yake bukatuwa da shi. Sannan kuma ta hanyar sanayya, abokantaka, taimakekkeniya, tattaunawa da canje-canjen tunani da manufofi, dan'Adamtakan mutum takan cika, haka nan ma samuwa da kuma bukatunsa na duniya da kuma na ruhi…. Alkur'ani mai girma ya bayyana mana wannan hakika, cikin fadinSa Madaukaknin Sarki cewa: "Ya ku mutane! Lalle ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da kabiloli domin ku san juna. Lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a takawa…." (Surar Hujurat, 49: 13) Ta haka ne rayuwar mutum ta kasance tausayi, soyayya da kuma taimakekkeniya …babu alheri cikin mutumin da ba ya son mutane haka su ma ba sa son sa. Sannan kuma a bangare guda irin wannan mummunan dabi'a ta gudun jama'a tana nuni ne da irin nakasi da kuma rashin yarda da kai da shi wannan mutumin yake fama da shi… Lalle mutum mai halin kaunar jama'a da kuma fara'a ga kowa, wanda kuma yake kokarin kulla alaka da sauran mutane, shi ne mutum wanda ya mallaki siffar yarda da kai kana kuma ma'abucin ingantacciyar dabi'a. Don kuwa shi yakan sami kansa cikin kwanciyar hankali da wadatuwar zuci cikin alakarsa ta abokantaka da sauran mutane a duk lokacin da yake nuna wa sauran mutane fuskar soyayya da yarda sannan su ma suke mayar masa da irin wannan siffa abin yabo. Mutum yakan sami kyakkyawar alaka da abokansa ne ta hanyar tattaunawar farin ciki, wasannin motsa jiki, karatu, taimakon abubuwan rayuwa, ayyukan taimakon jama'a, da dai sauransu…a daidai wannan lokacin mutum zai sami kansa cikin yanayin yarda da kai da kuma samun yardar Ubangiji da kuma sauran mutane. Sannan kuma ta hanyar abokantaka da abokan kirki zai samu damar samun kwanciyar hankali da daukakar ruhi. Kamar yadda aboki yakan amfana da wasu siffofinsu masu kyau na abokansa, da suka hada da karfinsu na kirkire-kirkire, ilimi da masaniya, haka su ma suke amfanuwa da shi ta hanyoyi daban-daban. A takaice dai ta hanyar wannan abota tasu za su iya amfanuwa da juna. Bugu da kari, ta haka zai iya amfanar da su ta ilimi da masaniyarsa, kyawawan halaye da tunace-tunacensa masu amfani, sannan kuma ta hakan kuma zai dinga jin kimar rayuwarsa da kuma yarda da kai. Don kuwa ta hanyar wannan alaka ta sa da sauran mutane zai iya fahimtar yanayinsa da kuma karfinsa na mu'amala da su da kuma irin tasirantuwan da zai yi da su da kuma samun karfin da yake bukatuwa da shi. Dukkan hakan zai sanya masa kwanciyar hankali da kuma yarda da kai. Hakika kimar ingantaccen yanayin mutum yana tabbata ne ta hanyar halaye da kuma irin amfanar da al'umma da ya yi, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya bayyana hakan cikin fadinsa cewa: "Mafi alherin mutane shi ne wanda ya amfanar da su (mutane) ( )". "Duk wanda mummunan aikinsa ya bata masa rai, kana kuma kyakkyawan aikinsa ya dadada masa rai, to mumini ne( )". Sannan kuma Imam Ali (a.s.) yana cewa: "Kimar mutum tana cikin abin da ya kyautata( )".
Ya Ya Za Mu Zabi Abokai
Hakika abokin mutum yana nuni ne da irin yanayinsa, a duk lokacin da mutane suka san yanayin abokin mutum, to sun san yanayinsa, haka nan ma a duk lokacin da suka san yanayin mutum, to sun san yanayin abokinsa…. masu iya magana sukan ce abokin barawo, barawo ne, kuma abokin mutum, abokinsa ne cikin tunani. Don kuwa mutum yana koyi da mutanen da yake tare da su cikin halaye da tunani ne. Don haka ne ma ya zo cikin wani hadisi mai tsarki cewa: "Mutum yana kan addinin (tunanin) masoyinsa, don haka ku binciki wanda za ku yi abota da shi( )". Abokantaka ita ce haduwa ta ruhi da kuma tunani wacce take hada tsakanin mutane da kuma haifar da ji-a-jika da kuma tausasawa tsakaninsu… Alkur'ani mai girma ya bayyana cewa 'yan'uwantakar da ta kasance karkashin asasin shiriya da amfanarwa, ita ce soyayya da kuma tausasawa tsakanin zukata, sannan kuma mai hada yanayi da kuma ruhin dan'Adam, kana kuma ya ambaci irin wannan 'yan'uwantaka da soyayya a matsayin babbar ni'ima ga dan'Adam… Allah Madakakin Sarki Yana cewa: "…Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku, a lokacin da kuka kasance makiya, sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku, saboda haka kuka wayi gari da ni'imarsa, 'yan'uwa…" (Surar Al'Imarana, 3: 103). Kana kuma Yana cewa: "…Idan da za ka kashe duk abin da yake bayan kasa gaba daya ba za ka iya hada zukatansu ba, amma kuma ga shi Allah Ya hade tsakaninsu…" (Surar Anfali, 8: 63). Wannan bayani na alakar 'yan'uwantaka da kuma soyayya da ake samu tsakanin mutane, a bisa asasin imani da ingantacciyar alaka, ita ce tsarkakakkiyar 'yan'uwantaka wacce babu wata cuta a cikinta. Bayanai da kuma kididdigogin da cibiyoyin kula da laifuffuka suka gudanar suna bayyana mana cewa munanan abokai (abokan da ba na kirki ba), ba abokai ba ne, face dai abokan gaba ne. Don kuwa a lokuta da daman gaske mummunar abokantaka takan sanya mutanen kirki cikin halayen banza da muggan laifuffuka. Alkur'ani mai girma yana tsoratar da mu kan yin abota da muggan abokai, don mu samu tsira daga nadama bayan wucewar lokaci. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Masoya a yinin nan, sashensu zuwa ga sashe makiya ne, face masu takawa". (Surar Zukhruf, 43: 67) Wannan kalami na abokin da yake nadaman zama da abokinsa ya kasance wa'azi da kuma darasi gare mu…haka kuma mun ga yadda abokantaka takan koma ta zama gaba da adawa da kuma fatan da ma mutum bai rayu da wannan mummunan aboki ba…. "Sai yace, "da dai a tsakanina da tsakaninka akwai nisan gabas da yamma, saboda haka tir da kai ga zama abokin mutum". (Surar Zukhruf, 43: 38). Don haka zaban aboki, a hakikanin gaskiya zabe ne ga irin nau'in yadda muke so yanayi da kuma mutumcinmu su kasance a idon al'umma, watakila ma muna iya cewa ga rayuwarmu ta nan gaba. Shin mutane nawa ne suka koma suka zama mutanen kirki ma'abuta nasara cikin rayuwa saboda abokansu, sannan kuma mutane nawa ne suka zama mutanen banza kana kuma suka bata rayuwarsu sabobda abokansu... Hakika babban kuskure ne mu kulla abokantaka da mutanen da ba mu san yanayin dabi'a da kuma halayensu ba. Me yiwuwa ne mu rudu da zahirinsu, ko kuma maganganunsu masu zaki, ko kuma da taimako da kyaututtukansu na yaudara gare mu, daga nan sai mu sami kanmu cikin abota da su abotar da ba za ta taba kuntuwa ba… Don haka dole mu ba da muhimmancin gaske da kuma kulawa ta koli wajen zaben mutanen da za mu yi abota da su bayan sani da fahimtar yanayinsu ta hanyar alaka ta makaranta, ko kuma a masallaci, ko rayuwa waje guda a gida guda, ko wajen aiki. Mai yiwuwa ne kuma mu sadu da wasu mutane yayin tafiya, ko kuma mutanen da suke bayyana kawukansu ta hanyar wasika, ta haka sai mu kulla alaka ta abota a tsakaninmu da su…to irin wannan nau'i na alaka, dole ne mu tabbatar da shi da kuma bincike sosai a kansa kafin mu kulla shi. Don kuwa irin wadannan mutane ba wai mun sansu sosai ba ne a farkon alakar tamu da su ba….a saboda haka dole ne mu zuba idanu sosai da kuma tunani kafin yarda da su.
Yadda Za Ka Kasance Abokin Kirki
Alaka da sauran mutane fanni ne daga cikin muhimman fannonin rayuwa ta zamantakewa, da yawa daga cikin mutane ba sa kyautata fannin alaka da sauran mutane…don haka ne suke fuskantar rashin nasara wajen samun abokai da kuma lalata alakarsu da sauran mutane. Hakan kuwa saboda ba su san yadda za su jawo hankalin mutane (abokai) zuwa gare su ba ne da kuma yadda za su yi mu'amala da su ba. Hakika ilmummukan sanin dan'Adam, na yau da kullum da kuma uwa-uba shiryarwa Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma tsarkakan Imamai (a.s.) duk sun koyar da mu hanyoyin samun abokai da kuma yadda za mu yi mu'amala da su…. Wadannan shiryarwa da kuma ilmummuka sun tabbatar mana da cewa mutum mai son kansa ba zai iya samun abokai ba, a duk lokacin da ya kulla wata alaka da wasu mutane ba da jimawa ba alakar za ta yi tsami saboda son kansa. Shi ba ya so musu abin da yake so ma kansa, haka nan ma ba ya ki musu abin da yake ki ma kansa, face dai dukkan kokarinsa shi ne shagaltar da su kan abubuwan da za su amfane shi kawai, don haka suke gudu daga gare shi. To amma a lokacin da aboki ya fahimci cewa abokinsa yana mu'amala da shi cikin soyayya da sadaukarwa da kuma kula da maslahohinsa a matsayinsa na abokinsa, ba makawa zai girmama shi, da kuma kokarin kara kyautata alakar da take tsakaninsu…. Don haka dole ka kasance maras son kai matukar kana son samun abokai…kana ka yi mu'amala da su cikin sadaukarwa…sadaukarwa kuwa ita ce gabatar da maslahar waninka a kan maslahar kanka a duk lokacin da ka fahimci yana bukatuwa da ita… Lalle Alkur'ani mai girma ya yabi irin sadaukar-war da Muhajirai (mutanen Makka) da Ansarawa (mutanen Madina) suka yi a tsakaninsu a matsayin-su na 'yan'uwa…don kuwa sun rayu rayuwa ta 'yan'uwantaka da abokantaka. An ruwaito cewa bayan hijirar Annabi (s.a.w.a.) zuwa garin Madina, mutanen Madina sun kasance sukan bai wa Muhajirai dukkan abubuwan da suke bukata na daga wajen zama, abinci, aure, tufafi, kai hatta ma ko da shi (mutumin Madinan) yana bukatuwa da wadannan abubuwa. Don haka ne Alkur'ani mai girma ya yabi wannan sadaukarwa da kuma jinjina wa Ansarawan saboda irin wannan taimako da suka yi wa Muhajirai suna masu neman yardar Allah…. Saboda girman wannan sadaukarwa da suka yi, har aka saukar da aya don jinjina musu, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Da wadanda suka zaunar da gidajensu (ga Musulunci) kuma (suka zabi) imani, a gabannin zuwansu, suna son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma basu tunanin wata bukata a cikin kirazansu daga abin da aka bai wa muhajirai, kuma suna fifita wadansu a kan kawukansu, kuma ko da suna da wata larura. Wanda ya saba wa rowar ransa, to, wadannan su ne masu babban rabo". (Surar Hashr, 59: 9).
Kyakkyawar Makwabtaka
Duk wanda yake so ya samu abokai kana su kuma su yi alaka da shi kamar yadda ya dace, dole ne ya makwabce su da kyau da kuma kyautata alaka da su. Daga cikin kyautata makwabtaka akwai cewa a duk lokacin da zai gana da mutane ya kasance mai sake musu fuska, mai murmushi yayin ganawa da kuma magana da su da dai sauransu, don kuwa hakan zai jawo kaunarsu gare shi. A daidai lokacin da fuska maras fara'a ta kan dada taimakawa wajen korar mutane daga gare ka, don haka dole ne mu guji turbune fuska yayin ganawa da mutane. Hakika murmushi da sakin fuska suna nuni ne ga kauna da kuma girmamawa, don haka ne suka zamanto hanyar jawo kaunar mutane ga mutum da kuma yada soyayya tsakanin mutane. Sakin fuskarka ga mutane da kuma fuskantarsu da maganganu masu dadi sukan bude zukatan mutane gare ka da kuma rufe kofofin kiyayya gare ka. Akwai wasu mutane da suke rayuwa cikin halin damuwa da kuma kumci, to amma a lokacin da ka yi mu'amala mai kyau da su da kuma sake musu fuska, za su sami sauki da kuma jin cewa ka damu da matsalar da suke ciki wacce suke neman mafita daga gare ta… Imam Sadik (a.s.) ya yi mana cikakken bayani kan wannan hali, inda yake cewa:"Murmushin mumini ga dan'uwansa mumini dabi'a ce mai kyau( ) ". Imam Muhammad Bakir (a.s) ma yana cewa: "Murmushi dabi'a ce mai kyau, sakin fuska yana jawo kauna da kuma kusanci ga Allah Madaukakin Sarki. Turbune fuska da kuma rashin murmushi kuwa yakan jawo kiyayya da kuma nesantar Ubangiji( ) ". Manzon Allah (s.a.w.a.) ma yana shiryar da mu yadda ake mu'amala da mutane don jawo hankalinsu da kuma samun nasara cikin mu'amala da su, inda yake cewa: "Lalle ba za ku iya samun kan (soyayyar) mutane da kudinku ba, ku dai ku yi mu'amala da su da sakin fuska da kuma murmushi(3) ". Don yada kyakkyawar mu'amala tsakanin mutane da kuma yaduwar soyayya da farin ciki, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana kiran mutane zuwa ga sakin fuska da kuma kyautata alaka. Yana cewa: "Allah Ya yi rahama ga duk wani mai sakin fuska da kuma saukin hali( ) ". Sannan kuma daga cikin hanyoyin samun nasarar jawo hankalin mutane da kuma samun abokai da tabbatar kyakkyawar mu'amala tsakanin mutane shi ne kyakkyawar magana. Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana mana irin gagarumar rawar da kyakkyawar maganar take takawa wajen kyautata alakokin mutane, inda yake cewa: "Kyakkyawar magana sadaka ce". Lalle kyakkyawar magana tana da nata tasiri mai girman gaske wajen samun nasara cikin mu'amala da mutane. Don kuwa a lokacin da abokinka ya ji kyakkyawar maganarka gare shi, zai nuna masa irin soyayyarka gare shi, ko kuma irin yadda kake son kyawun halayensa, ko kuma jinjinawarka ga irin kokarinsa da dai duk sauran kyawawan halayensa. A takaice dai wannan kyakkyawar magana takan bude kofar alakarka da abokinka da kuma jin girmamawa a tsakaninku, sai dai kuma yana da kyau mu kula kada mu wuce gona da iri wajen yabon mutane, don haka na iya sanya musu girman kai. Ko kuma wannan mutum mai kyakkyawan hali na iya canzawa zuwa ga mutum mai aiki don neman yarda da kuma yabon mutane ta hanyar wannan yabo da muke masa.
Ziyarce-Ziyarce Tsakanin Abokai
Daga cikin halaye da dabi'un da suka zamanto al'ada ga mutum shi ne ziyarar dangi, abokai da kuma makwabta a gidaje ko kuma wajajen ayyukansu…. Ziyara takan nuna wa mutumin da ka kai masa ziyarar irin damuwa, soyayya da kuma girmama-warka gare shi. Hakika ziyarar aboki, musamman ma a lokutan bukukuwan farin ciki, ko kuma na bakin ciki, rashin lafiya, bayan dawowa daga tafiya mai tsawo, yana nuni da kasantuwanka cikin dukkan halin da yake ciki da kuma taya shi murna ko jaje kan abin da ya same shi, a bangare guda kuma yana nuni da irin sadaukarwarka gare shi. A duk lokacin da aboki ya fara kai ziyara zuwa ga abokinsa ko kuma ya mayar masa da ziyarar da ya kawo masa yana kara dankon zumuncin da ke tsakani ne…. Ziyara kuma takan gyara alakar da ta yi tsami tsakanin abokai…don kuwa tana nuni ne da neman afuwa kan wani abin da ya faru da kuma nuna cewa abin da da yake a cikin zuciya na rashin yarda yanzu fa babu shi… A wasu lokuta a kan sami abokai suna ziyartar juna ta hanya cin abinci a guri guda, to hakan ma yana da tasirin gaske don yana nuni ne da yarda da kuma girmamawar da ke tsakanin juna… Lalle Allah Madaukakin Sarki Wanda Ya halicci mutum Yana son Ya ganshi yana da kyakkyawar alaka da sauran mutane, don haka shari'ar Musu-lunci ta kasance mai kwadaitar da musulmi kan kyautata 'yan'uwantaka, abokantaka da kuma ziyarce-ziyarce tsakanin 'yan'uwa da abokai… Sannan kuma Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana kiranmu zuwa ga ziyarar 'yan'uwa kana da kuma lada mai yawan gaske daga wajen Ubangiji. An ruwaito shi cikin wani hadisi yana cewa: "Babu wanda zai ziyarci dan'uwansa saboda Allah yana mai shaudin saduwa da shi, face Mala'ika ya kiraye shi daga baya cewa; ka sami babban rabo, sannan kuma Aljanna ta rabauta da kai( ) ". Imam Ja'afar Sadik (a.s.) yana cewa: "Hanyar sadarwa tsakanin 'yan'uwa a lokacin da ake gida ita ce ta hanyar ziyara, a yayin tafiya kuwa ta hanyar wasika( ) ". Imam Sadik (a.s.) din ya ruwaito cewa, Amirul Muminin (a.s.) yana cewa: "Ziyarar 'yan'uwa ganima ce babba, ko da kuwa ta yi kadan( ) ". Daga wadannan ruwayoyi da ma wasunsu, za mu fahimci muhimmancin da ke cikin ziyarce-ziyarce da kuma sadar da zumunta tsakanin 'yan'uwa da abokai. Duk da haka bari mu rufe wannan bayani namu da abin da aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s.) inda yake cewa; Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce: "Ziyara tana haifar da soyayya"; sannan kuma don kada ziyara ta rasa irin wannan muhimmanci nata, za mu ga Manzon Allah (s.a.w.a.) yana bayyana cewa ba ya kamata a sami lokaci mai tsawo tsakanin ziyara da wata ziyarar, sannan kuma kada ta kasance kullum, don kada a gaji da mutum. Annabi (s.a.w.a.) yana cewa: "Ka ba da lokaci tsakanin ziyara, sai soyayya ta karu".
Mummunan Makwabci Ba Aboki Ba Ne
Mai yiwuwa ne mutum ma'abucin halayen kwarai ya kasance ya kulla alaka ta abota da mutanen banza ta haka sai ya bata mutumcinsa saboda alakarsa da su. Matasa nawa ne ma'abuta kyawawan halaye suka koma ga aikata munanan ayyuka (suka zama mutanen banza) saboda zama da kuma alaka da munanan abokai. Suka koma mutanen banza masu cutar da mutane, marasa kunya… Don haka abokin banza ba aboki ba ne; don kuwa abokinka shi ne wanda yake tare da kai cikin alheri da kuma jan ka zuwa gare shi ta hanyar wannan abota taku. Amma duk wanda zai cutar da kai da kuma jan ka zuwa ga bata, aikata laifuffuka da kuma lalata maka makoma, ko kuma ka koyi munanan dabi'u a wajensa, ba aboki ba ne, don haka ne ma Alkur'ani mai girma ya ambace shi a matsayin makiyi, inda yake cewa: "Masoya a yinin nan, sashensu zuwa ga sashe makiya ne, face masu takawa". (Surar Zukhruf, 43: 67). Sannan kuma Alkur'ani mai girma yana mana bayanin halin nadama da mutum ya kan shiga bayan ya yi nisa cikin aikata laifi da kuma kauce wa hanya saboda abokantaka da muggan abokai… sannan kuma da yadda wannan mutumin zai yi kwadayin da ma ace bai san wannan aboki nasa ba, da kuma cewa da ma ace nisan da ke tsakaninsa da shi ya kai nisan gabas da yamma. Allah Madaukakin Sarki Yana siffanta irin wannan hali na nadama cikin littafinSa, cewa: "Da dai a tsakanina da tsakaninka akwai nisan gabas da yamma, saboda haka tir da kai ga zama abokin mutum". (Surar Zukhruf, 43: 38). Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Misalin abokin kwarai da abokin banza, kamar mai rike da turaren miski ne da mai hura zuga-zugi, don mai rike da miski, imma dai ya ja ka ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka shaki kamshi daga gare shi. Amma mai hura zuga-zugi, imma dai ya kona maka tufafi, ko kuma ka shaki wari daga gare shi( ) ". Kididdigan da wasu cibiyoyin kula da muggan laifuffuka suka fitar suna nuni da cewa da yawa daga cikin samaruka da matasan da suke shaye-shayen muggan kwayoyi, sata, kisan kai da dai sauran laifuffuka, sun koyi hakan ne ta hanyar abokantaka da masu irin wadannan muggan halaye, daga karshe rayuwarsu takan kare a cikin gidajen yari da kuma kyama irin ta al'umma. Da a ce ba su sadu da irin wadannan muggan abokai ba, da ba su sami kansu cikin irin wannan bala'i ba, da sun ci gaba da zamansu a matsayin yaran kirki. Bincike ya nuna cewa kashi 42 cikin dari na yaran da suka fada cikin tarkon muggan laifuffuka da bata, sun bayyana cewa abokansu su ne suka batar da su da kuma sanya su akan wannan tafarki. Sannan kuma kididdigar da aka gudanar kan masu shan muggan kwayoyi tana nuni da cewa kashi 43 cikin dari na wadannan mutane suna shaye-shayen ne saboda abotarsu da wadanda suke shan muggan kwayoyin ne. Hakika duk wanda ya girmama mutumcinsa, kana kuma ya kiyaye matsayinsa a cikin al'umma ba zai taba abuta da muggan abokai ba. Hakan kuwa yana kiran matasa maza da mata ne wadanda suke son zaben abokai, da su lura sosai wajen zaben mutanen kirki ma'abuta mutumci.
Kiyaye Sirri
Kowane mutum yana da sirrin da ya kebanta da shi, don haka dole ne ya kula da shi don kuwa shi wani sashi ne na mutumci da kuma rayuwarsa. Kada ya yada shi tsakanin mutane ya sa kansa cikin hatsari, watakila ma har da iyalansa… Mai yiwuwa ne mutum ya yarda da wasu mutane, ta haka sai ya gaya musu sirrorinsa da kuma wasu al'amurra da suka kebanta da shi kawai, wato ya sanya mutumci da kuma rayuwarsa a hannun wasu kenan….to a irin wannan hali ya zama wajibi ga su wadannan mutane da su kiyaye wannan sirrin. Kamar yadda masu iya magana suke cewa: magana zarar bunu, ko kuma cewa magana mallakarka ce, amma idan har ta fita daga gare ka, to ka zama mulkinta. A wasu lokuta mutum yana bukatuwa da ya yi shawara da wasu abokansa kan al'amurran da suka shafe shi shi kadai, don haka sai ya gaya musu don neman taimakonsu, ko kuma don ya tsoratar da su da ita. To a nan abin da ya hau kansu shi ne kiyaye wannan sirri don kuwa amana ce, saboda ya gaya musu ita ce don yardar da ya yi da su. To amma wasu mutane suna da dabi'ar yawan magana, ta yadda sukan gaya wa dukkan wani mutum da suka sadu da shi maganganun da ya shafe su, to lalle hakan yana da hatsarin gaske, dole ne a kiyaye shi. Wasu mutane kuwa suna da dabi'ar rike sirrin da ka gaya musu matukar dai alakarka da su tana nan da kyaunta, to amma a duk lokacin da suka sami sabani da kai, sai su bayyanar da wannan sirri naka. Ko kuma wasu mutane sukan canza daga yanayi mai kyau da aka sansu da shi zuwa mummunan yanayi, don haka sai su yi amfani da sirrinka da suka sani wajen cutar da kai da kuma tilasta maka biyan bukatun da suke so daga gare ka, idan kuwa ba haka ba sai su bayyanar da wannan sirri…. Daga cikin mutane kuma akwai wadanda ba sa iya rike sirri, kuma ba sa kiyaye wasa da mutumcin sauran mutane, daga lokacin da suka ji wata magana daga wajen abokinsu, Allah-Allah suke su gaya wa sauran mutane…. Da yawa daga cikin mutane sun fada tarkon yada sirrin mutane da kuma bayyanar da shi, inda mutumcinsu ya zube a idon jama'a ko kuma suka fada cikin wahala da wulakanci. Sirrin mutane, a wasu lokuta, yakan kasance ne cikin wani mummunan aiki da mutum ya aikata saboda jahilci da rashin saninsa…Allah Madaukakin Sarki Ya kan rufa wa bayinSa asirinsu, yafuwa da kuma gafarta wa masu neman gafara. Don haka a lokacin da mutum yake bayyanar da sirrinsa yana sa kansa da kuma mutumcinsa cikin hatsari ne, mai yiwuwa ma ya toshe hanyar tuba da kuma nesantar wannan muguwar dabi'a ce. Lalle hakan kuwa haramun ne, sannan kuma ha'inci da cutar da kai ne… Akwai hadisai da wasiyoyi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) da kuma Imamai (a.s.) da kuma ma'abuta hikima da suke kiranmu zuwa ga kula da sirrikan-mu. Ga kadan daga cikin irin wadannan wasiyoyi da kuma kalmomin hikima: "Sirrinka bawanka ne, idan har ka bayyanar da shi ka zama bawansa( )". "Bayyanar da sirri, halaka ce( )". "Kada ka gaya wa abokinka sirrrinka, sai dai abin da ko da makiyinka ya san shi ba zai cutar da kai ba, don mai yiwuwa ne wata rana abokinka ya zamanto makiyinka( )". Yana da kyau mu koyi darasi daga wadannan wasiyoyi da kuma hikima, don mu kula da harsu-nanmu daga yawan maganganu da kula da bayyanar da sirrorin da suka kebanta da mu. Sannan kuma kamar yadda muke son abokanmu su kiyaye mana sirrorinmu a duk lokutan da muka bayyana musu, haka mu ma ya zama wajibi mu kare da kuma kula da sirrori da kuma kura-kuransu. Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yana shiryar da mu zuwa ga wannan kyakkyawar dabi'a, inda yake cewa: "Duk wanda ya rufa wa dan'uwansa musulmi sirrinsa a duniya bai bayyanar da shi ba, Allah Zai rufa masa nasa sirrin a ranar lahira". "Duk wanda ya rufa wa dan'uwansa musulmi sirrinsa a duniya bai bayyanar da shi ba, Allah Zai rufa masa nasa sirrin a ranar lahira". Kamar yadda muka sani ne akwai wasu abubuwan da suke fitowa daga mutum wadanda da a ce mutane za su sansu da sun zamanto masa abin kunya da tozartarwa; don haka ne Allah Madauka-kin Sarki Ya umurce mu da rufe sirrori da kuma kura-kuren mutane. Abin da kawai ya hau kanmu a nan shi ne nasiha da shiryar da su ba tare da mun bayyanar da su ga sauran mutane ba.
Sadaukarwa Ga Aboki
Aboki shi ne wanda ya kasance mai sadaukarwa ga abokansa cikin farin ciki ko bakin ciki, cikin wahala ko jin dadi… Hakika daga cikin abokai akwai wanda alakarsa da kai takan rude ka, yakan kasance tare da kai da kuma yi maka fara'a da kuma kyautatawa matukar dai kana cikin wadata da jin dadi…amma a duk lokacin da ya lura kana cikin kunci, ko kuma kana bukatar taimakonsa, sai ya canza maka fuska, kamar babu wata alaka ta soyayya ko abokantaka da ta taba wanzuwa a tsakaninku. To irin wannan nau'i na abokai ba abokai ne masu sadaukarwa ba. Mutane nawa ne suka kasance tare da abokai da kuma mutane masu yawan gaske a lokacin da suke cikin jin dadin duniya, ko kuma suke mallakar wani matsayi mai girma, amma daga baya su watse musu a lokacin da dukiyar tasu ta kare ko kuma suka rasa wannan matsayi a gwamnati ko kuma a cikin al'umma, ko kuma a lokacin da suka wayi gari suna bukatuwa da taimakonsu, ko kuma suka gagara ba su taimakon da suka saba ba su. Tarihi ya bayyana mana misalan sadaukarwa da kuma 'yan'uwantaka. An ruwaito cewa wasu daga cikin musulman farko (masu suna Masruk da kuma Khaithama) sun kasance ko wannensu yana da bashi mai yawan gaske a kansa, kuma kowane daya daga cikinsu ya san bashin da ke kan dan'uwansa. Don haka sai Masruk ya dinga biyan bashin Khaithama, alhali shi kuwa (Khaithama) bai san da hakan ba, haka shi ma Khaithama a nasa bangaren ya dinga biyan bashi Masruk ba tare ya sani ba. Hakika irin wannan hali yana nuni ne da ainihin alaka ta abokantaka ta gaskiya, da kuma kasancewa cikin dadi da kuma wahala… Sannan kuma sadaukarwa ba ita ce kawai ka yi ta (sadaukarwar) ga abokinka kawai ba, a'a face ma har ga abokansa, 'ya'ya da kuma iyalansa…. Lalle kan daga cikin sadaukarwar gaskiya ita ce sadaukarwar Manzon Allah (s.a.w.a.). An ruwaito cewa matar Annabi (s.a.w.a.), uwar muminai Khadija (r.a) tana da kawayen da suke zuwa wajenta lokacin tana raye, to bayan rasuwarta, Manzon Allah (s.a.w.a.) ya kasance yakan tuna da su da kuma ba su kyaututtuka. Kuma idan ya yanka wata dabba yakan ce " Ku aika (naman) ga kawayen Khadija". Wata rana sai Ummul Muminina A'isha ta tambaye shi dalilin hakan, sai yace: "saboda ina son masoyanta ne". Don haka aboki shi ne wanda yake sadaukarwa ga abokinsa, kuma ba ya barinsa yayin bukata da kuma tsanani, sannan shi kuma ba zai mance da shi ba lokacin da ya sami wani matsayi ko kuma mukami.
Hakkin Nasiha
Abokinka shi ne wanda ya yarda da kai… lalle wannan wata hikima ce madawwamiya wacce abokai da kuma ma'abuta hankali suke amfani da ita…mazansu da matansu…. Hakkin aboki ne a kan abokinsa da ya yi masa nasiha, don kuwa kowane mutum yana bukatar nasiha daga sauran mutane, kamar yadda kuma yake bukatar shiri wajen karbar nasihar da aka yi masa…. Hakika ilimi da masaniyar mutum suna da iyaka... sannan kuma akwai wasu abubuwa a tare da mutum wadanda a wasu lokuta su kan tura shi zuwa ga alheri, kana kuma a wasu lokuta zuwa ga sharri. Bugu da kari kuma a rayuwa akwai wasu mutane ashararai wadanda suke karfafa mutum da kuma tunkuda shi zuwa ga sharri, tabewa da kuma muggan dabi'u…. Babu shakka matukar dai mutum ya rasa mai masa nasiha da kuma shiryar da shi, ba makawa yana iya fadawa cikin hatsari…da dai sauransu. Don kuwa mutumin da ilimi da masaniyarsa ba su cika ba, yakan fada cikin hatsari a lokuta da dama, don haka yana bukatar wanda zai ba shi shawarwari da nasihohin da za su taimaka masa wajen samun nasara wajen zaben irin aikin da zai yi, ko kuma kasancewa cikin ayyukan zamantakewa, siyasa, ko kuma na tattalin arziki, ko kuma wajen zabin abin da zai karanta a makaranta, ko kuma a lokacin da yake tunanin neman aure…da dai sauransu. Daga cikin hakkin abokinka shi ne yin masa nasiha da kuma ba shi ilmummukan da ka ke da su wadanda za su taimaka masa da kuma amfanar da shi; don ya bar wani abin da ya ke aikatawa matukar dai akwai cutarwa a cikinsa ko kuma wata matsala wacce bai riga ya fahimce ta ba. Ko kuma ka kwadaitar da shi aikata wani abin da ka ke ganin akwai amfani da kuma maslaha gare shi, ko kuma ka taimaka masa da cikakkiyar masaniya kan wannan lamari, don ya taimaka masa wajen aikin ko kuma wata matsalar da yake fuskanta a rayuwarsa, kamar karatu, aure, neman aiki, saye da sayarwa ko kuma alaka da mutane cikin wani aiki na musamman. Idan har ka bar abokinka ba tare da nasiha ba, kana shi ma ya bar ka ba tare da nasiha ba, to lalle ka ha'ince shi kana shi ma ya ha'ince ka…don kuwa aboki aminin abokinsa ne kuma mai sadau-karwa ne gare shi…. Mai yiwuwa ne nasiha ta tsamar da mutum daga halaka da kuma kauce wa hanya, kamar yadda kuma wasu nasihohin sukan ceto mutum cikin rayuwarsa ta karatu, siyasa, zaman iyali, tattalin arziki da kuma na zamantakewa. A wasu lokuta muhimmancin nasiha takan kasance wajiba a kanmu, sannan kuma Allah Zai tambaye mu da kuma hukumta mu idan har mu ka bar nasiha ga abokanmu har wata cutarwa ta same su. Addininmu na Musulunci ya kasance mai umurtanmu da yin nasiha ga 'yan'uwa da abokanmu; hakan kuwa ya zo cikin hadisi cewa: "Nasiha ga mumini tana wajaba cikin abubuwan da aka gani da ma wadanda suka buya( ) ".
Tsawatarwa Da Kuma Gargadi Tsakanin Abokai
Alaka tsakanin abokai takan kasance na tsawon shekaru ko watanni, watakila har tsawon rayuwa… to a tsakanin wannan lokaci ana iya ganin dabi'u da halaye kala-kala tsakanin abokan masu amfanarwa da kuma masu cutarwa….sannan kuma kuskure dabi'a ce ta mutum, babu wani wanda ba ya kuskure a cikin mutane (in ban da Wadanda Allah Ya tsarkake). Mutum yana yin kuskure a alakarsa da Ubangijinsa, da kansa da kuma sauran mutanen da yake rayuwa da su. Sanannen abu ne cewa duk wanda aka saba masa zai mayar da martani kan wannan sabawa da aka yi masa…sannan kuma mayar da martanin ya kan bambanta gwargwadon irin nau'i da kuma girman kuskuren, kana kuma da irin yanayin mutumin da aka yi masa kuskure, karfinsa na hankali da kuma dabi'arsa wajen mu'amala da kura-kuren da mutane suka yi masa. Wasu sukan yi tsananin fushi da kuma fadin muggan maganganu ga wadanda suka aikata kuskure gare su, wasu kuwa sukan yi shiru kan kuren da kuma rufe idanu da kuma kunnuwan-su kamar ba su ji ko gani ba, kana kuma sukan yafe a dukkan halaye, komai girman irin kuren da aka yi musu. Mu'amala tare da kura-kuren abokai suna da asasi na kyawawan halaye…don kuwa a duk lokacin da wani aboki ya yi kuskure ga abokinsa, misali ya gaya masa wata magana mai cutarwa ko kuma ya yi masa wasa da dukiya da dai sauransu, to daga cikin hakkin aboki shi ne ya gargade shi kan wannan kure nasa, to amma dole ne wannan gargadi ya zamanto da kyautatawa da kuma nusar da shi kan kuskurensa. Don kuwa hakuri da kuskuren da ke faruwa daga mutane al'amari ne na asasin rayuwar abokai, duk wanda ba ya hakuri da kura-kuren mutane, ba zai iya rayuwa da su ba. To amma wanda yake wuce haddi da kuma cutar da abokansa, to ba ya kamata su rike shi a matsayin aboki gare su. Suna iya bayyanar masa da kurensa, amma ta hanyar da ta dace. Hakika Alkur'ani mai girma yana kiranmu ga afuwa ga wanda ya saba mana, da kuma gargadin mutanen da suka saba mana amma ta hanyar da ba zai cutar da mutumcinsu ba. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "…kuma suke masu hadiyewar fushi, kuma masu yafewa mutane laifi. Kuma Allah Yana son masu kyautatawa". (Surar Al' Imrana, 3: 134). "…kuma ku fadi magana mai kyau ga mutane". (Surar Bakara, 2:83). "Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa, kuma ku fadi magana madaidaiciya". (Surar Ahzabi, 33:70). Hakika nuna rashin jin dadi da kuma gargadi ga wanda ya saba, lamari ne da yake da kyau kana kuma ma wajibi saboda gyara kuren da aka yi da kuma ci gabantar da alakar da ke tsakani abokai. To amma sai dai kuskure ne nuna rashin jin dadi a kan dukkan kananan kura-kure ko kuma idan nuna rashin jin dadin zai kai ga cin mutumci da kuma wulakanta abokin naka. Dole ne mu kula da girmama mutumcin abokanmu. Lalle idan har muna son abokinmu ya karbi nuna rashin jin dadinmu da kuma kokarin gyara kuren da ya yi, to mu ma dole mu yarda da hakan idan ya fito daga gare shi. Sannan kuma mu bude zukatanmu da hankulanmu ga karbar hakan, don kuwa mutum ma'abucin kuskure ne, amma nuna rashin jin dadi ta hanyar da ta dace yakan sa shi ya gyara kura-kuran nasa.