Drawer trigger

Adalci Da Daidaitawa

   ADALCI DA DAIDAITAWA A baya yayin da muke magana kan wannan batu mun bayyana cewar sun samo asali ne daga akidar wajibcin adalci da haramcin zalunci, da kuma cewa mafi bayyanar misdakin adalci cikin alaka ta zamantakewa shi ne daidaitawar mutum a kan kansa. Haramcin Zalunci Haramcin zalunci bai takaita kawai ga mutum ya aikata (wani aiki na) zalunci ba, face dai dole matsayar mutum ta kasance mai kin zalunci ne a dukkan bangarori. Muna iya ganin hakan cikin wadannan al’amurra masu zuwa: a)– Mayar da Abin Da Kwace Idan wani ya zalunci wani mutum na daban, misali ya kwace masa dukiyarsa, ko kuma ya kwace ko take masa wani hakki daga cikin hakkoki, idan daga baya ya tuba, to dole ne ya mayar da abin da ya kwace daga wajen mutumin da ya zalunta, wannan shi ne ake kira da ‘mayar da abin da aka kwace (zalunta). Abu Ja’afar (a.s) yana cewa: “Zalunci uku ne: zaluncin da Allah ke yafewa (gafatarwa), da zaluncin da Allah ba Ya yafe shi, sai kuma zaluncin da Allah ba Ya barinsa. Zaluncin da Allah bai yafe shi, shi ne shirka, shi kuwa zaluncin da Allah ke yafe shi, shi ne zaluncin da mutum ke yi wa kansa cikin abin da ke tsakaninsa da Allah, amma zaluncin da Allah bai barinsa shi ne zaluncin da mutum ya yi wa sauran mutane[1]”. Daga Wahab bn Abdur-Rab, da Ubaidullah al-Tawil, daga wani dattijo daga dattawan al-Nakh’ yana cewa: “Na gaya wa Abi Ja’afar (a.s): Na kasance gwamna tun lokacin Hajjaj har zuwa yau din nan, shin zan iya tuba (za a iya karbar tuba ta)?, sai ya ce: sai Imam ya yi shiru, sai na sake masa wannan tambaya sai ya ce: A’a, har sai ka mayar wa masu hakki hakkokinsu (da ka take)[2]”. Daga Abi Basir yana cewa: “Na ji Aba Abdullah yana cewa: Duk wanda ya ci dukiyar dan’uwansa cikin zalunci kuma bai mayar masa ba, to ya ci garwashin wuta a Ranar Kiyama[3]”. Haka nan idan ya zalunci wani zalunci na ma’anawiyya kamar giba (cin nama – yi da wani a bayansa), cin mutumci, kazafi da dai sauransu da za mu ambato su nan gaba, don haka ya zama dole ya yi kokarin mayar da wannan hakki tare da neman gafara daga wadanda ya zalunta – bayan neman gafara daga wajen Ubangiji Madaukaki – da neman gafara da ayyuka na kwarai gare su da mutumta su da dai sauran abubuwan da ake daukansu a matsayin mayar da hakki ga wadanda aka kwace. b)– Shiriya Bayan Bata Mai yiyuwa daya daga cikin mafi bayyana da girman nau’in zalunci na ruhi ga sauran mutane shi ne batar da su daga hanya madaidaiciya da tura su zuwa ga bata, idan har mutum ya gano haka ya kuma tuba, to dole ne ya yi kokarin shiryar da su zuwa ga gaskiya da komar da su zuwa gare ta. Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Akwai wani mutum a zamanin farko da ya nemi duniya ta hanyar halal amma bai samu ba, ya nema ta ta haramun bai samu ba, sai Shaidan ya zo masa ya ce: Ashe ba zan nuna maka wani abin da za ka iya samun duniya da shi ba, sannan kuma ka kara yawan nemanka? Sai ya ce: Na’am, sai ya ce masa: Ka bi duniya da kuma kiran mutane zuwa gare ta, sai ya aikata hakan jama’a kuma suka bi shi, ya kuma samu duniya, daga baya sai ya yi tunani yana mai cewa: shin me na aikata ne? na kirkiro wasu abubuwa na duniya na kuma kira mutane zuwa gare ta, babu lokacin da zan so tuba face sai wani daga cikin wadanda na kira ya zo ya mayar da ni, ta yadda har ya kan je wa mutanen da ya kiraye su yana ce musu: abin nan da na kiraye ku gare shi karya ce, ni na kirkire shi, su kuwa sai su ce masa: ina, karya kake yi gaskiya ce, face dai kai ne ka ke cikin shakku kan abin da kake kai, sai watse su bar shi. Lokacin da ya ga haka sai ya ya nemo sarka ya daure wuyansa da ita, yana cewa: ba zan taba kunce ta ba har sai Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta mini. Sai Allah Ya yi wahayi wa daya daga cikin AnnabawanSa Ya ce masa: Ka gaya wa wane cewa: Da daukakaTa da za ka ci gaba da rokona har…ya yayyanke ba Zan gafarta maka ba har sai ka dawo da wanda ya mutu a kan abin da ka kiraye shi gare shi da dawo daga wannan tafarki[4]”. c)– Taimakon Zalunci Kamar yadda ya haramta mutum ya aikata zalunci da kansa, haka nan ya haramta masa ya taimakawa azzalumi cikin zaluncinsa, ko kuma ya kasance daga cikin masu taimakon azzalumai bisa fahimtar da mahangar al’umma. Daga Abdillah bn Sanan yana cewa: “Na ji Aba Abdullah yana cewa: Duk wanda ya taimaki wani azzalumi wajen zaluntar wanda aka zalunta zai ci gaba da zaman cikin fushin Ubangiji har sai ya janye wannan taimako nasa[5]”. Daga Amirul Muminina (a.s) yana cewa: “Azzalumi daga cikin mutane na da wasu alamu uku: zai zalunci wanda ke samansa da sabo, wanda ke kasansa kuma da gabala zai kuma bayyanar wa al’umma da zalunci[6]”. Daga Aliyu bn Husain (a.s) cikin wani hadisi yana cewa: “Ina gargadinku da zama da masu sabo da kuma taimakon azzalumai[7]”. Daga Ja’afar bn Muhammad daga Iyayensa (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: A Ranar Kiyama wani mai kira zai yi kira: ina masu taimakon azzalumai, da wanda ya ba su tawada, ko kuma ya kulle musu jaka, ko kuma ya mika muku alkalami? Ku tayar da su tare da su[8]”.

d)– Yarda da Zalunci da Shiru Kansa

Kamar yadda ya haramta mutum ya aikata zalunci da kansa, haka nan ya haramta gare shi ya yarda da kuma yin shiru kan zalunci. Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Mai aikata zalunci da mai taimaka masa da kuma wanda ya yarda da hakan ‘yan’uwan juna ne (wajen aikata zalunci)[9]”. Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Duk wanda ya yarda (uzuri) da zaluncin mai zalunci, Allah Zai dora masa wanda zai zalunce shi a kansa, idan kuma ya yi addu’a ba za a karba ba, Allah ba Zai saka masa kan zaluncin da aka yi masa ba[10]”. Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Duk wanda ke fatan wanzuwar azzalumai, to lalle ya so ya ci gaba da sabawa Allah[11]”.

Misdakin Adalci da Daidaitawa Tsakanin Mutane

A bangaren adalci da daidaitawa mutum ga sauran mutane, za mu ga Ahlulbaiti (a.s) suna mana nuni da wasu abubuwa da ke tabbatar da hakan, baya ga abin da muka yi ishara da shi na daga ‘son mumini ga dan’uwansa mumini abin da yake so wa kansa’:

a)– Sakayya da Alheri

Daga cikin hakan har da sakayya da alheri da abu mai kyau da aka yi wa mutum da kamansa ko kuma wanda ya fi shi, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ke fadi cikin littafinSa mai tsarki: ﴾ هَلْ جَزَاء الإحْسَانِ إلا الإحْسَان ﴿ “Shin, kyautatawa na da wani sakamako? Face kyautatawa[12]”. Haka kamar amsa sallama ne da kamarsa ko kuma abin da ya fi shi, kamar yadda ke cewa: ﴾ وَإِذَا حُيِّيْتُم بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّواْ بِأَحْسَنَ مِنْهَا أَوْ رُدُّوهَا ﴿ “Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta ko kuwa ku mayar da ita[13]”. Akwai hadisai masu tsarki da suka zo da jaddadawa kan batun sakayayya da alheri. Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Amirul Muminina (a.s) yana cewa: duk wanda ya saka da gwargwadon abin da aka yi masa, hakika ya mayar da abin da aka yi masa ne, idan kuwa ya rubanya shi ya kasance godiya, wanda ya gode ya zama karimi, duk wanda ya san cewa duk abin da ya aikata ya aikata ne ga kansa ba zai yi saibi ba wajen gode wa mutane, ba zai ki bukatarsu su kara cikin kaunarsu ba, kada ka roki waninka godiya kan abin da ka yi wa kanka, ka kuma kare mutumcinka. Ka san cewa wanda ke bukatar wani abu a wajenka ba zai karamta fuskansa daga fuskanka ba, don haka ka karamta fuskarka daga mayar masa[14]”. Daga Aliyu bn Salim yana cewa: “Na ji Aba Abdullah (a.s) yana cewa: Akwai wata aya da aka rubutata sai na ce: wace aya kenan? Sai ya ce: ﴾ هَلْ جَزَاء الإحْسَانِ إلا الإحْسَان ﴿ da ta hau kan mumini da kafiri, mai da’a da fajiri; duk wanda aka yi masa wani abu na alheri to ya saka da shi, sai sakawar ba ita ce ya mayar da abin da aka yi masa ba, face dai ya ga cewa wanda ya aikata masa hakan yana da falalar farawa[15]”. Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Allah Ya la’anci mai tare hanyar alheri! Sai aka ce masa wane ne kuma mai tare hanyar alheri? Sai ya ce: shi ne wanda aka aikata alheri gare shi amma ya kafirce wa hakan, ya kuma hana mai aikata alherin aikata shi ga waninsa[16]”. Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: duk wanda aka yi masa alheri ya saka da shi, idan kuwa ba zai iya ba to ya gode da shi, idan kuwa bai aikata haka ba to ya kafirce wa ni’ima[17]”. b) – Mayar da Hakkoki Daga cikin hakan har da mutum ya san hakkin dan’uwansa kamar yadda dan’uwan nasa ya san hakkinsa, saboda hakkoki tsakanin muminai abu ne na musanye, kamar yadda za mu iya ganin hakan cikin wasu hadisai da aka ruwaito daga Ahlulbaiti (a.s) kan hakkin mumini. Daga ciki har da abin da aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Ashe ba zai kasance abin kunya ba ga wani daga cikinku idan makwabcinsa ya san (kiyaye) hakkinsa, amma shi bai san hakkin makwabcin nasa ba[18]”. c) – Shagaltuwa da Aibin Kai da Mantawa da Aibin Wasu Daga cikin hakan har da shagaltuwa da aibin mutum da kokarin gyaransa da kuma rufe ido kan aibobin sauran mutane. An ruwaito Abu Ja’afar al-Bakir (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Siffofi uku, duk wanda ke da su ko kuma guda daga cikinsu zai kasance karkashin inuwar al’arshin Allah a ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa: mutumin da ya ba biya wa mutane bukatunsu alhali yana bukatuwa da abin, da mutumin da bai taba gabatar da wani mutum ko jinkintar da wani ba har sai ya san akwai yardar Allah cikin hakan da kuma mutumin da bai taba aibanta dan’uwansa musulmi kan wani aibi ba har sai ya kawar da wannan aibi daga jikinsa, saboda ba zai kawar da wani aibi ba sai ya sake ganin wani aibin, ya isar wa mutum ya shagaltu da kansa daga mutane[19]”. Daga gare shi (a.s) yana cewa: “Ya isa ya zamanto aibi ga mutum ya fahimci aibin mutane da zai sanya shi rufe ido kan lamurran kansa, ko kuma ya aibanta mutane kan wani abin da yake tattare da shi da zai iya mai da shi ga waninsa ba, ko kuma ya cutar da abokin zamansa da abin da bai shafe shi ba[20]”. d) – Fadin Alheri Kan Mutane Daga ciki har da fadin alheri kan mutane gwargwadon abin da mutum yake so a fadi kansa, da suka hada da kyakkyawan zato da daukan maganganu da ayyukan mutane bisa mafi kyaun fuska (zato), da kuma godiya da yabonsu. Daga Abi Ja’afar (a.s) cikin fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: “Ku fadi alheri kan mutane” yana cewa: “Ku fadi dangane da mutane abin da kuka fi a fadi dangane da ku[21]”. Dukkan wadannan abubuwa za su iya kasancewa karkashin babin adalcin mutane ga kawukansu.
[1] . Wasa’il al-Shi’a 11:342, hadisi na 1. [2] . Wasa’il al-Shi’a 11:342, hadisi na 3. [3] . Wasa’il al-Shi’a 11:342, hadisi na 4. [4] . Wasa’il al-Shi’a 11:343, hadisi na 1. [5] . Wasa’il al-Shi’a 11:345, hadisi na 5. [6] . Nahjul Balaga, hikima ta 350. [7] . Wasa’il al-Shi’a 12:128, hadisi na 1. [8] . Wasa’il al-Shi’a 12:130, hadisi na 11. A wannan babi akwai hadisai da yawa makamantan wannan da muka yi ishara da wasu daga cikinsu a baya. [9] . Wasa’il al-Shi’a 11:345, hadisi na 1. [10] . Wasa’il al-Shi’a 11:345, hadisi na 2. [11] . Wasa’il al-Shi’a 12:134, hadisi na 5. [12] . Suratur Rahman 55:60. [13] . Suratun Nisa’ 4:86. [14] . Wasa’il al-Shi’a 11:536, hadisi na 1. [15] . Wasa’il al-Shi’a 11:537, hadisi na 3. [16] . Wasa’il al-Shi’a 11:539, hadisi na 1. [17] . Wasa’il al-Shi’a 11:539, hadisi na 2. [18] . Wasa’il al-Shi’a 8:399, hadisi na 4. [19] . Wasa’il al-Shi’a 8:228, hadisi na 1. [20] . Wasa’il al-Shi’a 8:229, hadisi na 3. [21] . Wasa’il al-Shi’a 11:563, babi na 21, hadisi na 3.