MACE DA WAYEWAR DUNIYANCI

MACE DA WAYEWAR DUNIYANCI

Karanta tarihin al'ummu da kasashe a tsawon zamunansu, yana fito mana da wahalhalun mace, kuntata mata da takura mata. Babu wani tsari ko akida da ya yaye wa mace mayafin zalunci da kuntatawa in ba ka'idojin Allah da suka hadu da mafi kyawun surarsu a sakon Musulunci madawwami ba. Kafin mu bayar da bayani game da kimar mace, hakkokinta da matsayinta mai ban sha'awa a Musulunci, yana da kyau mu kawo wasu alkaluman kididdiga wadanda ke magana a kan wahalhalun mace da masifun da ta sha a karkashin wayewar duniyanci na zamani karkashin jagorancin Amirka da kasashen Turai, wadanda ke daga taken 'hakkokin mace'. Alkaluman kididdiga na ta'akidi a kan cewa, dan Adam din da ya ji jiki a karkashin wannan wayewa, kuma ya zama bawa da na'urar jin dadi shi ne: Mace. Ga wasu daga cikin alkaluman kiddidiga na cewa:­ "Wani rahoto da kamfanin dillacin labaran kasar Faransa ya kawo ya bayyana cewa: kashi 70 bisa dari na mutane biliyan 1.3 da ke raye a cikin halin mugun talauci a duniya su ne mata, kuma akwai kimanin mata biliyan 2.3 da ba su iya karatu da rubutu ba a duniya. Haka nan kashi uku bisa hudu na daukacin matan kasashen Norway, Amirka, Holland da Newzaland na fuskantar hare-haren fyade. A Amirka kuwa, cikin kowadanne dakikoRi 8 mace daya na fuskantar mummunar mu'amala; haka cikin kowadanne dakikolti 6 ana sace mace daya"8 Rahoton ya kara da cewa:­ Kimanin mata rabin miliyan daya ke mutuwa a kowace shekara saboda ciki da suka dauka da cutukan shi, kuma kimanin kashi 40 bisa dari na wannan adadi yan mata matasa ne. Kuma albashin mata miliyan 828 da ke aiki a fagagen tattalin arziki ya fcaranta daga albashin maza da abin da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa kashi 40 bisa dari, kuma irin dan tagazawar nan na bankuna da ake ba ma'aikata a duniya ba sa samun fiye da kashi 10 bisa dari na wadannan agaje-agaje".9 Haka nan ya zo cikin wani rahoton cewa:­ "A bisa wani bincike da ma'aikatar adalci ta kasar Amirka ta aiwatar, an gano cewa adadin sace mutane ko yunkurin sace mata na faruwa a Amirka har sau 310 a kowace shekara, wannan kuwa ya ninka alkaluman da hukumar 'yan sandan cikin Amirka ta F.B.I. ta bayar."lo Kuma kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga Washigton ya bayar, a kowace shekara akwai halin yi wa mata fyade har sau rabin miliyan a Amirka; alhali kuwa hukumar 'yan sanda ba ta bayar da sanarwar adadin samuwar sace (mata) ko yunkurin sace su a Amirka ba face dubu 140, kamar yadda alkaluman kididdigar hukumar F.B.I. ya bayyana. Haka nan ya zo cikin wani rahoto da jaridar kasar Iran mai suna lddila'at ta bayar a adadinta na 20,401 daga kamfanin dillancin labaran Iran da ke birnin Rom na kasar Italiya, cewa:­ "Matsalar halayyar rashin tausayi na kara matufcar tsananta a tsakanin iyalan Italiyawa, domin halin kashe iyaye a hannun `ya'ya da kashe 'ya`ya a hannun iyaye ya karu fiye da yadda ya kasance a da can. Haka wata jaridar Kasar Italiya, a adadinta na baya-bayan nan, ta dauko wani rahoton Kididdigar shekara-shekara na kungiyar Eruospas cewa: cikin watanni goman farkon na shekara ta 1994, an rubuta halin rashin tausayi har 192 a cikin iyalan Rasar Italiya, wadanda 129 daga wannan adadi suka Kare da kisa. Kamar yadda wannan rahoto ya nuna, irin wannan nau'i na rashin tausayi a shekara ta 1993 adadin shi ya kai 112, wanda kusan wannan adadin ya kare da halin kashe-kashe. wani abu, da ya zama dole a nuna shi ne cewa kimanin kashi 40 bisa dari na laifuffukan iyali ya faru ne a arewacin Italiya, kuma kashi 40.8 bisa dari daga cikinsu sun faru ne a kudancin kasar, alhali kashi 16.1 bisa dari ya faru a tsakiyar kasar. Kuma mafi yawan kashe-kashen iyali da aka yi a shekara ta 1994 sun faru ne a lardin Lombardi da ke arewacin Italiya". Haka nan jaridar 'Jumhuri Islami', a adadinta na 4,485, fitowarta shekara ta 1994, ta bayar da rohoton cewa:­'Mujallar Epidemiology (ilimin annoba) da ke Karkashin hukumar lafiya ta duniya (WHO), a adadinta na 11, na shekara ta 1993 ta rubuta alkaluman Kididdiga na karshe da ya Kunshi adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki (AIDS) a duniya baki daya, inda aka rarraba alkaluman daidai da yankunan duniya dabam-dabam. Alkaluman na nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki da suka tabbata ga wannan hukuma har zuwa shekara ta 1993, ya kai kimanin 718,893. Kimanin 371,086 na wannan adadi na wadanda suka kamu da cutar Kan jiki sun fito ne daga nahiyar Amirka, yayin da kimanin 247,577 suka fito daga nahiyar Afrika, kimanin 92,482 kuwa sun fito ne daga nahiyar Turai, adadin da ya kai 4,188 sun fito ne daga Australiya, 3,561 kuwa daga nahiyar Asiya. Wan aka bi kasa-Kasa kuwa, Kasar da ta fi kwasan adadi mai yawa ita ce Amirka, wadda ta kwashe adadin wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta kimanin 289,320, sai kuma kasar Tanzaniya da ke biye mata da kimanin 38,719, sai Kasar Birazil mai 36,481, sai Kenya da 31,185, sai Uganda mai 34,611, sai kuma Biritaniya mai 26,955, sai Faransa mai 24,226, sai kuma kasar Zaire mai 21,008, sai Spain mai 18,347, sai Italiya mai 16,860, sai Congo (Brazavill) mai 14,655, daga nan sai sauran kasashe su biyo baya. Kamar yadda za a iya lura, ba kawai kasar Amirka na matsayi na daya ba ne ta fuskar adadin wadanda suka kamu da cuta mai karya garkuwa jiki, a'a har ma akwai sabani mai yawan gaske tsakanin ta da Kasashen da ke biye mata. Kuma idan muka dauki wadannan alkaluma na adadin dari, za mu sami wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta a kasar Amirka sun kai kashi 40 bisa dari na dukkan wadanda suka kamu da ita a kasashen duniya 150, wannan kuwa duk da cewa adadin mazauna Amirka bai wuce kashi 5 bisa dari na dukkan al'ummar duniya ba'. Haka nan ya zo cikin wani rahoto da jaridar Ittila'at ta kasar Iran ta kawo, a adadinta na 20,482, fitowarta ta 21 ga watan Maris na shekara ta 1995, daga wakilinta a Madrid ta kasar Spain, inda yake cewa:­ "A shekara ta 1995 kashi 72 bisa dari na Rananan yara na raye ne a KarKashin ubanninsu, amma yanzu kimanin kashi 60 bisa dari daga cikinsu suna raye ne ba tare da ubanni ba. Yawan saki da fitinun uwaye sun sa maza sun gudu daga gidaje. Marubucin nan dan Kasar Amirka (David Blanc Horn), bayan ya bayyana wadancan alKaluman Kididdiga a cikin wani littafi na shi, ya kuma bayyana cewa: "Samun iyaye maza na gari na buKatar samun kyakkyawan misali na mata (wato yana bukatar samun mata na gari), wannan shi ne dalilin gudun iyaye maza daga gidajensu a Amirka.' Haka nan wakilin jaridar Faes ta Fcasar Spain, a wani rahoto na shi da ya bayar daga Amirka, ya bayyana cewa: Himmatuwa mai yawa da matan Rasar Amirka ya kare da cutar da ubanni da haramtawa `ya `ya inuwar ubanninsu". A wani rahoto da jaridar Itiila'at, a adadinta na 20,407, fotowar ranar 31 ga watan Yulin shekara ta 1995 ta dauko daga ofishin kamfanin dillancin labaran Iran (IRNA) da ke London game da yanayin da kananan yara ke cikin a Biritaniya, am bayyana cewa:­ "Majalisar Dinkin Duniya, a wani rahoto nata, ta yi kakkausar suka a kan yanayin da yara ke ciki a Biritaniya, da kuma dokoki da tsarin lura da yara a wannan kasa. Rahoton, wanda hukumar kiyaye hakkokin yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, ya nuna cewa dokokin da ake amfani da su a kan abin da ya shafi lafiya da ilimin kananan yara da shigar da su cikin al'umma a Biritaniya, ba a yi la'akari da cewa ya wajaba dokokin su lura da amfanonin yaran ba. Masana a hukumar kiyaye hakkokin yara ta Majalisar Dinkin Duniya na ganin cewa dokokin da suka kebanci kananan yara a Biritaniya sun fi mayar da hankali a kan yin ukuba da kulle yara da balagaggun matasan da suka karkace. Daga cikin wuraren da ake suka a cikin wannan rahoto akwai karuwar yawan kananan yara da ke rayuwa cikin halin talauci a Biritaniya, da karuwar alkaluman rabuwar aure, da raguwar tallafin hukuma ga matalautan iyalai, da karuwar yawan yara da samari da ke sake suna kwana a tituna. Haka nan masu rubuta rahoton sun bayyana damuwarsu da mummunar mu'amala da amfani da miyagun kwayoyi da fyade da ke fuskantar kananan yara. Kamar yadda majiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana, rahotannin majalisar game da yanayi kananan yara a kasashen Sweden, Norway da Denmerk sun yi soke-soke kamar irin na rahoton kasar Biritaniya". Haka nan ya zo cikin jaridar Jumhuri Islami, a adadinta na 4,485 cewa:­ "Ofishin kamfanin dillancin labaran Jumhuriyar Musulunci ta Iran a Born (ta fcasar Jamus) ya bayyana rahoton hukumar kidaya ta kasar Jamus (a shekara ta 1993) na cewa: adadin `ya `ya mata da ubanninsu ke tarbiyyantar da su su kadai yana ci gaba da karuwa a kowace shekara. Rahoton ya kara da cewa: A halin yanzu akwai kimanin uwaye mata dubu 455 a jihohin Jamus ta gabas (wato kashi 12 bisa (Tari na jimillar uwaye mata da ke wadannan jihohi ke nan) da ke tarbiyyantar da ya yansu su kadai. A gefen wannan kuma, daga uwaye mata miliyan 7 da ke jihohin Jamus ta yamma, kimanin dubu 915 (wato kashi 12 bisa dari) na uwaye matan suna daukar dawainiyar tarbiyyar 'ya `yansu su kadai. Da wannan ke nan zai zarna akwai kimanin uwaye mata miliyan daya da dubu 370 a tsakanin uwaye miliyan 9 da dubu 260 da ke tarbiyyar 'ya`yansu su kadai a tarayyar Jamus. Kamar yadda wannan rahoto ya nuna, kashi 46 bisa dari na wadannan uwaye a gabashin Jamus, da kashi 30 bisa dari daga yammacinta duk ba su yi aure na shari'a ba; kashi 43 bisa dari na wadannan uwaye kuwa mazajensu sun sake su, kasancewar kuma rike 'ya’ya a hannun uwaye mata yake, ya zama musu dole su dauki dawainiyar tarbiyyarsu. Haka nan a kasar Jamus akwai fiye da uwaye mata miliyan 9.26 da suka haifi 'yaya alhali shekarunsu na haihuwa bai kai 18 ba, kuma miliyan 5.4 daga cikinsu ko da yaushe ko rabin lokutansu suna ayyuka ne a wajen gida, banda kuma ayyukansu na gida da ayyukan tarbiyyar yara. Wani abu da ya kamata a bayyana a nan shi ne cewa yawan halin rabuwar aure a halin yanzu ya ninka yadda ya kasance a shekara ta 1968, wato ya karu daga dubu 65 da ya kasance a shekara ta 1968 zuwa dubu 135 a ‘yan shekarun nan, kuma a kowace shekara ana rijistar aurarraki dubu 390 a kasar Jamus, wadanda kashi 33 bisa dari daga cikinsu ke karewa da rabuwa, har ma wannan adadin a manyan garuruwa irin Hanburg ya kai kashi 50 bisa dari". Har ila yau jaridar Ittila'at a adadinta na 20,503 ta dauko wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da kamfanin dillacin labaran Iran (IRNA) ya kawo kamar haka:­ "Taimakon kasar Amirka ga hukmar (UNICEF), bai kai na kasa daya daga cikin kasashe 20 masu arzikin masana'antu a duniya ba. Bankin kula da Kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ma ya tabbatar da haka, ya kuma kara da cewa: Duk da Amirka da ke bayar da taimakon dala biliyan 9.7, ita ke martaba ta biyu bayan Kasar Japan wajen taimakawa hukumar UNICEF, wannan adadin kudi kuwa ba komai ba ne face kashi .15 bisa dari din kudaden shiganta, alhali kuwa Rasar Holland da sauran kasashen yankin Sakandanebiya su ke marhala ta daya a wannan fagen; domin taimakonsu na kaiwa kahi 8 bisa dari na kudaden shigansu. Shugabannin hukumar UNICEF sun nuna damuwarsu a kan raguwar taimakon da kasashe masu zarafi ke yi ga matalautan kasashe, har ma sun kara da cewa: 'Wannan abu na faruwa ne a daidai lokacin da rnuhimmancin taimakawa wajen kyautata lafiyar Kananan yara da kyautata yanayin ayyukan uwaye mata ke Karuwa a matalautan kasashe da tsananin gaske kuwa.' Kuma kamar yadda wannan rahoton ya nuna, a kowace shekara Kananan yara kimanin miliyan 13 a duniya ke mutuwa saboda cututtukan gudawa, bakon-dauro da sauransu. Haka nan kimanin Kananan yara miliyan 200 ke fama da rashin abinci mai gina jiki irin su vitamin A, abin da ke haifar musu da makanta!". Har ila yau ya zo cikin jaridar Ittila'at, a adadinta na 20,370, fitowar ranar 15 ga watan Disamban shekara ta 1994 cewa:­ "Kamfanin dillancin labaran Jumhuriyar Musulunci ta Iran (IRNA) daga Tehran ya bayar da labarin samuwar kananan yara kimanin rabin miliyan wadanda suka tarwatse a Amirka, a wasu lokuta ana aje su a wajen neman gina marayu, abin da al'ummar Amirka ke dauka a matsayin Kaskanci garesu. Wata marubuciya a jaridar Washintog Post mai suna Suzan Phildaz, ta rubuta cewa: 'Da yawa daga kananan yaran da ke da majibinta wadanda ke raye a karkashin iyalan da ke taimakonsu, suna fuskantar duka, wulakanci da mummunan mu'amala, kai! a wasu lokuta ma ana kashe su.' Har ila yau Phildaz na cewa: 'Nau'in mu'amalar kowace al'umma tare da 'ya'yanta wata muhimmiyar alama ce da ke nuna hakikanin wannan al'umma.' Har ila yau ta kara da cewa: Adadin kananan yara da ke watse sai kara yawa yake yi a Amirka kullum, har ta kai ga a wasu lokuta `yan sanda na gano jarirai a wuraren tara juji. A irin wannan hali taimakon uwaye mata na kudade ba ya wadatarwa, maimakon haka, babu makawa a samar da wasu cibiyoyi don amsa manyan bukatun wadannan kananan yara." Hafiz Muhammad Sa’id Kano Nigeria.