TAKAI TACCEN TARIHIN ANNABIN TSIRA (SAWW)

Bai kasance yana magana ko kira zuwa ga wani takamammen yare ko wata kabila ba, a'a ya tsaya ne don taimakon 'yan Adam ba tare da la'akari da Kabila, launi, matsayi, yare ko kuma inda suka fito ba. Sakon da yake isarwa cikakken sako ne wanda ya kore duk wani abin da zai kawo cikas ga rayuwar mutane. Cikakken sako ne wanda ba kawai ya canza zamanin da aka saukar da shi ba ne, a'a muna iya ganin haskensa da shiriyar da ke cikinsa hatta a wannan zamani. Kai, wannan wane irin saKo ne! kuma wane ne ya zo da wannan sako? Shin zai iya magance matsalolin wannan zamani (tare da irin ci gaban kimiyya na wannan zamani)? Shin zai iya biya wa mutum buKatunsa musamman ma mutumin wannan zamani? Shin yana da amsoshi ga bukatun dan'Adam na yau da kullum? Shin zai iya zaburar da masana wajen binciken kimiyya? Ina kuma batun kyawawan dabi'u? Shin shi wannan mai sako (Manzo) yana aikata abin da yake fada ko kuwa kawai yana cikin wadanda suke fadan abin da ya yi mugu dadi ne kawai? To 'na'am' ita ce am sa ga duk wadannan tambayoyi da aka yi a sam a da ma wasu tambayoyin daban; ma'ana wannan sako zai iya magance duk wadannan matsaloli. Ba wai kawai jin dadin rayuwar duniya ba, har ma muna iya samun jin dadin rayuwar lahira idan muka yi riko da gaskiya da wannan sako da kuma tafarkin wanda ya zo da sakon. In da mutum zai yi watsi da son zuciyarsa, to da zai iya gane cewa wannan Sako wanda ake kira Musulunci da kuma Annabi na Karshe mai suna Muhammadu, ba wai kawai amfaninsu ta taKaita ga larabawan karni na sha hudu da suka wuce ba ne, a'a suna iya magance rikitattun matsalolin wannan zamani wanda ake kira da zamanin kimiyya (zamani na ci gaba). Wannan kalma ta Islam (Musulunci) daga Salam (zaman lafiya) take, wadda a 'Istilahance' take nufin mika wuya; wato mika wuya ga Allah Wanda Ya halicci wannan duniya Ya kuma halicci dan Adam a bisa mafi kyan halitta, kuma Ya azurta shi da karfin tunani. Kai wannan abin mamaki ne domin shi wannan mika wuya yakan tsamar da mutum daga mika wuya ga gumaka, wasu ra'ayoyi da wasu camfe-camfe. Me za mu iya rubutawa a kan mutumin da ya canza mahangar duniya, sannan kuma ya ceci dan Adam daga bata! Wannan abu a fili yake idan muka yi la'akari da cewa shi din nan Allah ne Ya zabe shi don isar da wannan sako, cikakken mutum ne wanda hatta makiyansa sun gagara gano kure (kome kashinsa) a cikin rayuwarsa. Yaya za mu yi da mutumin da Alkur'ani ya siffanta shi da 'abin kayi' ga mutane (har ma da wadanda za su zo nan gaba). A fili yake cewa Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya tara siffofi na gari kamar hakuri, jarumtaka, hikima, karimci, basira da dai sauran su, wadanda suka zama abin koyi a gare mu. Saboda kwadayin ilmantar da mutane gaskiyar Musulunci da kuma wane ne Manzon Allah ya sa mu ke farin cikin kaddamar muku da wannan dan karamin bincike dangane da rayuwar wannan fiyayyen halitta (Muhammadu s.a.w.a). Muna fatan masu karatu za su ji dadin wannan aiki kuma su amfana da shi. Daga karshe muna rokon Allah da Ya karbi ayyukanmu. Amincin Allah Ya tabbata a gare ka Ya Manzon Allah, ranar da ka aka haife ka, ranar da ka yi wafati da kuma ranar da za a tashe rayayye kana mai ceton wadanda suka yi riko da tafarkinka. Yanayin Larabawa Kafin Aiko Annabi (s) Larabawa a wancan lokacin -na jahiliyya- ba su kasance ma'abuta littafi ko mabiya wani saukakken addini ba, balle har -littafin ko addinin- ya daga matsayinsu na tunani, zamantakewa da wayewa. Jahilci da duhun kai da karkacewa ne kawai suka mamaye tsibirin larabawa, kuma suke wasa da hankula da akida. Larabawa sun kasance suna bautar gumaka, aljanu, taurari da Mala'iku; kadan daga cikin su ne suka kasance a kan addinan Annabi Ibrahim, Musa da Isa (a.s). A irin wannan halin al'ummun da suka fi labarawa wayewa da ci-gaba, wato Yahudawa, Nasarawa da Majusawa, suka kasance. Su ma sun kasance karkashin kamun rayuwar jahiliyya, bata da karkacewar akida da zaluncin siyasa. Suna karkashin masu dagawa. Akwai wasu manyan dauloli uku da ke kewaye da larabawa. Akwai daular Rum daga yamma, daular Farisa daga gabas, sai daular Habashawa daga kudu. Wadannan su ke da karfin siyasa da wayewa a wancan lokacin. Kasancewar larabawan da ke garin Makka da kewaye ba su san ma'anar hukuma ba, sun kasance suna raye karkashin mulkin kabilanci da shugabancin wasu manya masu karfi a kan talakawa da bayi. A irin wannan duhun zamantakewa, mace ta kasance tana dandana rayuwar wahala da rashin mutunci. Ba ta da hakki, ba daraja; saboda ita, a al'adar wannan al'umma ta jahiliyya, mallakar namiji ce, ana gadon ta kamar yadda ake gadon dabbobi da abubuwan mallaka. 'Ya'ya sun kasance suna gadon matan ubanninsu kuma su aure su. Dayan su ya kasance idan aka haifar masa 'ya mace sai bakin ciki ya rufe shi, ya shiga tsoron kunyata da bacin suna, sai ya dauki matakin kashe ta ko bisne ta da rai ko ya karbeta cikin wulakanci da kiyayya. Yayin da muka fahimci wannan hakika, za mu iya fahimtar Musulunci da girman Annabinsa (s.a.w.a); wanda, bisa yardar Allah, ya iya ceto dan Adam da sanya shi a kan hanyar madaukakiyar wayewa da daidaituwar dabi'a da shiriya. Hakika Allah Madaukaki Ya siffanta sakon AnnabinSa da fadarsa cewa: Hakika haske ya zo muku daga Allah da littafi mabayyani. Da shi, Allah na shiryar da wanda ya bi yardarsa tafarkin tsira, kuma yana fitar da su daga duhu zuwa haske da izinin Shi, kuma Yana shiryar da hanya madaidaiciya. (Ma'ida: 15-16)  

Haihuwar Mai Albishir, Annabi Muhammadu (s)

(A bisa ingantattun ruwayoyi), an haifi Manzon Allah (s) ne a ranar 17 ga watan Rabiul Awwal, ko da yake wasu ruwayoyin sun ce ran 12 ga wanann wata ne, a garin Makka, a shekarar da ake kira da Shekarar Giwaye. Dalilin da ya sa ake kiran wannan shekara da haka kuwa shi ne wani gwamnan Sarkin Abbasiniya ne mai suna Abrahata ya shigo Makka da runduna mai yawa bisa kan giwaye (bayan ya kame garin Yaman) da nufin rusa Dakin Ka'aba da sauya alkiblar mutane zuwa San'a (domin a wancan lokacin mutane sukan kawo ziyarar bauta a Ka'aba) inda da ma tuni ya gina wani guri don wannan ziyara. Amma daga baya lokacin da Abrahata ya iso Makka da wannan runduna ta sa, sai Allah Ya aiko da wasu irin tsuntsaye dauke da tsakuwoyi a bakunansu, inda suka rinka jefo wadannan tsakuwoyi a kan wadannan runduna, nan take suka kashe sojojin da giwayen. Ta haka ne Allah Ya yi maganin wannan azzalumi da mutanensa. Mahaifinsa dai shi ne Abdullah dan Abdul Mutallibi dan Hashim; Mahaifiyarsa kuwa ita ce Amina 'yar Wahb, Kakansa kuwa shi ne Abdul Mutallibi, wanda ya kasance yana da 'ya'yaye da yawa, amma Abdullahi (mahaifin Annabi) da Abu Talib (mahaifin Imam Ali) mahaifiyarsu guda ne. Don haka ya fito ne daga cikin madaukakin gidan nan na Bani Hashim wanda ya fito daga kabilar Kuraishawa wadanda ke da dangantaka da Annabi Isma'il (a.s) dan Annabi Ibrahim (a.s). Manzon Allah (s) dai ya tashi ne a matsayin maraya saboda kasancewar mahaifinsa ya rasu yayin da ya kai ziyara Yathrib (Madina) watanni uku kafin haihuwar Manzon Allah (s). Tattare da bakin cikin rasuwar Abdullah, amma haihuwar wannan maraya ta sanya iyalansa, Amina da Abdul Mutallib, cikin farin ciki da ba shi da iyaka. Sun shirya gagarumar walima ga 'yan'uwa da makwabta, inda aka yi yanka don murnar wannan haihuwa. A sakamakon haka duk Makka ta dauki murna, inda mutane suka yi ta zuwa gidan Abdul Mutallib don mika sakon taya murna gare shi. A bisa al'adar mutanen Makka, sukan kai 'ya'yayensu shayawar kauye saboda samun kyawawan dabi'dabi'u da kuma yanayi mai kyau da dai sauransu, don haka an aika da Muhammad (s.a.w.a) wajen da Halima 'yar Abi Zu'aib al-Sa'adiyya a kauye don shayar da shi. Hakika Halima ta sadu da alhairai masu yawa daga abin shayarwarta Muhammad (s.a.w.a). Lokacin da al-Mustafa ya cika shekaru shida da haihuwa sai Halima ta dawo da shi zuwa Makka, yayin da ya sami kakansa Abdul-Mudallibi a matsayin mafi alherin mai reno gare shi; domin ya kasance yana ba shi duk abin da yake bukata na tausayi da kauna irin ta iyaye masu lura. Ya kasance yana ba shi matsanancin kulawa fiye duk daukacin iyalin shi. A shekara ta shida da haihuwarsa sai mahaifiyarsa ta tafi da shi ziyarar danginsa na nono, wato banu Udaiyyu bin Najjar a Yathrib (Madina), a tare da su akwai Ummu Aiman. Sai suka saura a can har na tsawon wata daya, sannan sai suka juyo suka kama hanyar dawowa Makka. A hanya ne ajali ya samu mahaifyarsa Amina, aka bisne ta a Abwa, wanda wani gari ne da ke tsakanin Makka da Yathrib (Madina). Sai Ummu Aiman ta dawo da shi wajen kakansa, yayin da ita kuma ta dauki nauyin aikin uwa, kamar yadda kakansa Abdul-Mudallibi ya dauki aikin uba. Wannan kulawa dai ba ta jima sosai ba don shi ma wannan kaka nasa Allah Ya dauki ransa a lokacin Mustafa na da shekaru takwas da haihuwa. Daga nan sai kulawarsa ta koma hannun Baffansa Abu Dalib , wanda ya yi mu'amala da shi da kauna, sassauci da lura irin ta iyaye, ta yadda babu wani daga 'ya'yansa da ya sami irin hakan. Ya kasance yana barci a shimfidar Baffansa, yana zama gefen shi, yana cin abinci tare da shi, yana fita tare da shi duk lokacin da ya fita daga gidansa; da wasun wadannan na daga nau'o'in lura da so wadanda irin su ke da wuyan samu. Muhammad (s.a.w.a) ya kasance yana girma a hannun Baffansa alhali daukakan halayensa na girma tare da shi, ta yadda har sai da ya kebantu da wasu siffofi na nagarta a tsakaninsa da mutanensa da suka hada da gaskiya, rikon amana, daidaito da halin girma; wadannan siffofi dai sun kebanta da shi ne ban da waninsa; har ma ta kai ma mutanen suna kiransa da "Mai Gaskiya da Rikon Amana". Ganin cewa dai ya fara girma kuma don kada ya zauna haka, Muhammad al-Mustafa (s.a.w.a) ya fara aiki a lokacin yana matashi. Aikin da ya fara yi shi ne kiwon tumaki/awaki. Sannan sai ya bi Baffansa Abu Dalib zuwa Sham don kasuwanci. A wannan lokaci ma dai Manzon Allah (s) ya nuna fasaha, kwazo, gaskiya da kuma rikon amana a wannan fage lamarin da ya jawo hankalin wata hamshakiyyar attijira mai suna Khadijah bint Khuwailid zuwa gare shi. Don haka sai ta nemi shi da ya kula mata da wani sashi na kasuwancinta, ta ba wasu dukiya mai yawan gaske don gudanar da kasuwanci, wanda daga karshe ta samu riba mai girman gaske da ba ta taba samu ba.  

Auren Manzon Allah (s) Da Khadijatul Kubra (a.s)

A lokacin da ya cika shekaru ashirin da biyar da haihuwa sai ya tafi kasar Sham don gudanar da kasuwanci da wannan dukiya da Khadija bint Khuwailid (r.a) ta ba shi, inda kamar yadda muka bayyana a baya aka riba mai girman gaske da ba a taba samun irinta, hakan kuwa saboda albarkar da ke tattare da Annabin ne da kuma irin gaskiya da rikon amanarsa. Wadannan abubuwa dai sun faranta wa Khadijah rai kwarai da gaske da kuma kaunar Annabin. Khadija dai ta kasance daga zababbun matan Kuraishawa kuma ta fi su kudi da kyau. An haife ta ne a garin Makka kuma a can ta girma, tun a lokacin jahiliyya ana kiranta da "Tahira" (tsarkakakkiya), saboda irin kyawawan halaye da take da su a tsakankanin matayen Kuraishawa. A lokacin da ta ba wa Manzon Allah (s) dukiyarta don kula mata da su wajen kasuwanci, Khadijah ta hada shi da wani amintaccen yaronta mai suna Maisara. Irin kyawawan halayen Manzon Allah (s.a.w.a) dai sun yi tasiri wa Maisara, don haka sai ya tafi wajen Khadiza yana gaya mata irin dabi'un Muhammad (s.a.w.a) da ya gani, wannan ya sa son Manzo ya shiga zuciyarta, sai ta bukace shi da ya aureta, ya zama mijinta, alhali kuwa ta ki amincewa da manyan Kuraishawa wadanda suka zo neman auren nata. Manzo (s.a.w.a) dai ya amince da wannan bukata ta Khadijah, inda ya aureta, inda suka tabbatar da mafi kyaun kusanci da ake iya mafarki, wanda ya kyautatu da kauna, alkawari da tausayin juna; suka shata mafi kyawun sura na rayuwar auratayya mai nasara. Bari mu ji wata hikaya daga Ammar bn Yasir wanda ya kasance abokin Annabi ne tun suna yara kan yadda aure nasu ya kasance da kuma yadda aka daura shi. Ga abin da Ammar din ya ke cewa: "Ni nafi kowa sanin auren Manzon Allah (s) da Khadijah bint Khuwailid; don na kasance abokin Ma'aiki (s). Wata rana muna tafiya tare da Manzon Allah (s) tsakanin Safa da Marwa sai ga Khadijah bint Khuwailid tare da 'yar'uwarta Hala. Lokacin da suka ga Manzon Allah (s) sai Hala ta ja ni gefe ta ce min: 'Ya Ammar! Abokinka ba shi bukatuwa (da auren) Khadijah? Sai na ce: 'Wallahi ban sani ba. Sai na koma na gaya masa. Sai ya ce min: "Koma ka sa mana lokacin da za mu je mu gana da ita....sai kuwa na koma na aikata hakan (wato muka sa rana). Da ranar ta zo.....sai Manzon Allah (s) ya zo da baffanninsa karkashin jagorancin Abu Talib, inda ya karbi aurenta a hannun baffanta Amru bn Asad, kasantuwan mahaifinta, Khuwailid bn Asad ya rasu. Bayan gama bukuwan aure, sai Manzon Allah (s) ya koma gidan Khadijah da zama, wannan gida da ke da dimbin tarihi wajen ci gabantar da musulunci da kuma taimakon marasa galihu. A yayin zamansu dai, Khadijah ta kasance mace mai tsananin biyayya ga mijinta da kuma taimaka masa a dukkan bangarorin rayuwarsa, kamar yadda shi ma ya kasance hakan tare da ita. A lokacin da aka aiko shi a matsayin annabi, ita ce mace ta farko da ta fara imani da shi, ta karbi wannan kira nasa, ta ba da dukkan abin da ta mallaka don Allah da kuma ci gabantar da wannan addini. Babu makawa, dole ne Manzon Allah (s) ya saka mata saboda irin wannan hidima da ta yi masa da kuma addinin Allah, don haka ya kasance mai tsananin sonta, girmama ta lokacin tana raye da ma bayan rasuwarta (a.s), saboda matsayin da take da shi a cikin zuciyarsa. Irin wannan kulawa da matsayi na Khadijah dai ya sa Annabi (s) bai auri wata mace a lokacin tana raye ba, ko da bayan rasuwarta lokacin da ya yi aure ya kan yawan tunawa da ita, har ya kan ce ita ce matan da ya fi so cikin dukkan matansa. A'a ya ya kuwa ba zai fadi haka ba, alhali kuwa ita ce ta tsaya kyam tare da shi a lokacin yunwa, talauci da wahalhalu wadanda mushirikan Makka suka dora masa, kuma ga ta ita ce uwar dukkan 'ya'yansa, in ban da Ibrahim. An ruwaito cewa, bayan rasuwarta, a duk lokacin da ya yanka wani abin yanka, ya kan dauki wani bangare na naman ya ce: "Ku aika wannan wa kawayen Khadijah'. An ce wata rana A'isha, matar Manzon Allah, ta tambaye shi me yasa yake haka: sai ya ce mata: "Saboda ina sonta". Haka nan ma an ruwaito cewa wata mace ta zo wajen Manzon Allah (s), a lokacin yana dakin A'isha. Nan take ya tashi ya karbe ta hannu bibbiyu ya gaggauta biya mata bukatan da ta zo nema. Wannan lamari ya ba wa A'isha mamaki, sai ta tambaye shi dalilin hakan, sai ya ce mata: "Ta kasance tana zuwa gurinmu lokacin rayuwar Khadijah". Har ila yau kuma an ruwaito A'ishan dai tana cewa: 'Wata rana Manzon Allah (s) zai fita daga gida, sai ya tuna da Khadijah, ya fadi wasu kalmomi na girmamawa gare ta. To amma sai na gagara rike kai na sai na ce masa; 'Ita dai ba wani abu ba ne face tsohuwar mace, kuma a halin yanzu Allah ya musanya maka wadanda suka fi ta'. Nan take Manzon Allah (s) ya mayar mata da martani, cikin fushi yana cewa: "Lallai ba haka ba ne...lalle ban samu wadanda suka fi ta ba. Don kuwa ita ce ta yarda da annabcina a lokacin da kowa ya kyale ni. Ta ba ni dukkan dukiyarta a lokaci mafi tsanani (na bukatuwa da su). Kuma Allah Ya ba ni zuriya ta hannunta, alhali kuwa ya haramta min daga wasunta". Khadijah ta ci gaba da taimaka wa Manzon Allah (s) har lokacin da Allah Ya karbi ranta a shekara ta goma bayan wahayi, wannan rasuwa nata dai ya kasance babban abin bakin ciki ga Manzo (s), bugu da kari kuma kan rasuwar Baffansa kana kuma mai kare shi Abu Talib (a.s), don haka ma ya kira wannan shekara ta sunan Shekarar Bakin Ciki.  

Saukar Wahayi Ga Manzon Allah (s)

Ko da yake mutanen garin Makka suna girmama Manzon Allah (s) saboda kyawawan dabi'unsa, amma shi ya gwammacewa kadaita da nisanta kansa daga wannan mushirikar al'umma; ya kan tafi wani kogo a wajen Makka wanda ake kira Kogon Hira, don bautar Allah, tunanin girmanSa da kuma nisanta daga munanan ayyuka da suka zama ruwan dare a Makka. Da farko ya kan zauna a kogon na tsawon yini guda zuwa kwanaki biyu, wani lokaci ma har kwanaki goma; amma kusan saukan wahayi ya kan zauna har na tsawon wata guda don bautar Allah da kuma tunanin yadda za a shiryar da wannan lalatacciyar al'umma. A lokacin da ya cika shekaru arba'in da haihuwa, kamar yadda ya saba, yana cikin wannan kogo na Hira inda yake shagaltuwa da ibada, kwatsam sai ya ga Mala'ika Jibrilu (a.s) ya bayyana gare shi da ayoyin farko na Alkur'ani: Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta. Ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu da (Sunan) Ubangijinka mafi girma. Wanda Ya sanar da mutum (ta hanyar) alkalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba. (Surar Alak:1-5) Da wadannan ayoyi, Mala'ika Jibrilu (a.s) ya sanar da Annabi (s) cewa Allah Ya zabe shi a matsayin ManzonSa na karshe ga talikai. A dalilin haka, Muhammadu (s) ya kasance cikin matukar farin ciki da godiya ga Allah saboda wannan baiwa da Ya yi masa, saboda haka ya gaggauta komawa gida don sanar da matarsa Khadija wannan baiwa ta zabarsa a matsayin Annabi. Sai ya kwanta a gadonsa don ya dan sami hutu. A wannan lokacin ne kiran daga Allah a karo na biyu ya zo gare shi: Ya kai mai lulluba. Tashi ka yi gargadi. Ubangijinka kuma ka girmama Shi. Tufafinka kuma ka tsarkake su. Gumaka kuma ka kaurace musu (Mudassir:1-5) Wannan kira ne na tafiya da sako da yin albishir da sabon addini da daukar da'awar Allah zuwa ga mutane. Don haka ba abin da ya ragewa Manzon Allah sai amsa kira da gaggauta sanar da Ali bin Abi Talib(1). (a.s), wannan da jahiliyya bata gurbata shi da dattinta ba, kuma bai taba sujjada ga gunki ba. Domin ya tashi ne a hannun Manzo (s.a.w.a) kuma a gidansa. Sai ya amsa kiran Allah, ruhinsa ya rungumi ruhin sakon Allah Madaukaki. Kamar yadda kuma Manzo ya bijirar da da'awarsa ga matarsa Khadija, ita ma sai ta amsa kiransa ta yi imani da sakonsa. Da wannan aka hada wani gungu na al'umma mumina a doron kasa, wanda ya kumshi Muhammad, Ali da Khadija. Da wannan dalili, Khadija da Imam Ali (a.s) suka kasance wadanda suka fara musulunta (Khadija ta bangaren mata Ali kuma a bangaren maza). Ta haka ne aka saukar da wannan sako na Musulunci wanda ba wai kawai zai tsarkake Larabawa daga daudar shirka ba ne, a'a har ma haskensa zai haskaka duk duniya baki daya. Sai Manzo (s.a.w.a) ya ci gaba da kira a boye yana samun amsawa, har adadin wadanda suka yi imani da wannan sako ya karu. Don cika tanajin na kololuwa, sai Manzo ya shiga koyar da su Alkur'ani da hukunce hukuncen sakon, kamar yadda kuma suka dinga yin salla wararen da suka nisanta daga idanuwan mutane. Yayin da adadin muminai ya yawaita har suka fara jin tsoron tonuwar al'amarinsu, sai suka mayar da gidan Arqam al-Makhzumi ya zama wajen karatu da shiri da ibada. ____________ (1)- Ahmad bin Hambali cikin Masnad, juzu'i na 2, shafi na 368; da Hakim cikin al-Mustadrik, juzu'i na 4, shafi na 336; da Ibin Athir cikin al-Kamil, juzu'i na 2, shafi na 22; da littafin al-Isti'ab, juzu'i na 2, shafi na 459; da wasun wadannan.  

Matakan Manzon Allah Wajen Isar Da Sako

Haka dai shekaru yayi ta wucewa da'awar Musulunci na ci gaba da yaduwa, duk kuwa da kokarin da Kuraishawa suka yi wajen dakushe sakon, bayan da labarin bayyanar wannan sabon addini, amma dai hakan ya ci tura don sai jama'a ne suke ta ka musulunta. Don haka muna iya kasa kiran da Annabi ya yi a Makka zuwa kashi biyu, wadanda kowannensu yana da na sa rawar da ya taka, su ne kuwa kamar haka:
  1. Da'awar Sirri.
  2. Da'awar Sarari.
DA'AWAR SIRRI Saboda irin adawar da kafiran Makka suke nunawa wa Musulunci, Manzon Allah (s) ya kasance ya kan kira mutane zuwa ga Musulunci ne a boye. A dai dai wannan lokaci sai Allah Ya hore shi da ya kira na kurkusa da shi daga cikin danginsa, don kuwa a lokacin wadanda suka yi imani da shi ba su wuce mutane arba'in ba. Allah Madaukakin Sarki Ya ce masa: Kuma ka gargadi danginka na kusa. Ka kuma tausasa ga wanda ya bi ka daga muminai. Idan kuwa suka saba maka, sai ka ce: 'hakika ni na barranta daga abin da kuke aikatawa. (Surar Shu'ara':214-216) Sai Manzo (s.a.w.a) ya gayyaci danginsa cin abinci. Fara kiransa ke da wuya sai baffansa Abu Lahabi ya yanke shi, ya tsawatar da shi a kan ci gaba da kiran. Sai taro ya watse ba tare da Manzo ya sami daman ci-gaba da kiransa ga mutanensa ba. A karo na biyu ma dai ya sake tara su, bayan cin abinci ya gabatar musu da wannan sako, a wannan karon ma dai bai samu nasarar isar da abin da ya ke son isarwa, saboda tarwatsa taron da Abu Lahb din ya sake yi. Sai a karo na uku ne Manzon Allah ya sami damar yin magana, inda bayan da aka gama cin abinci, sai ya mike kafin Abu Lahb din ya ce wani abu ya fara da cewa: Ya ku 'ya'yan Abdul-Mudallibi, lallai Allah Ya aiko ni gare ku da sako na masamman, sai Ya ce: "Kuma ka gargadi danginka na kusa." To ina kiran ku ne zuwa ga kalmomi biyu masu sauki ga harshe (amma) kuma masu nauyi a mizani: Shaidawa babu abin bauta sai Allah, kuma ni ManzonSa ne. wane ne zai amsa min wannan al'amari ya kuma taimake ni a kan aiwatar da shi, sai ya zama dan'uwana, abin wasicina, mataimakina, mai jiran gadona kuma Khalifana a baya na?(1). Babu dai wani da ya amsa masa daga cikin dangin nasa in ban da Ali bn Abi Talib (a.s), alhali kuwa shi ne ya fi kowa karancin shekaru a gurin, inda ya mike ya ce wa Manzon Allah (s)Ni zan taimake ka a kan wannan al'amari. Sai Manzon Allah (s) ya umarce shi da ya zauna, inda ya sake maimaita wannan bukata tasa, amma dai babu wani wanda ya amsa masan in ban da wannan saurayi Ali (a.s), a wannan karon ma dai Annabin ya ce masa ya zauna. Sai da aka yi haka har sau uku amma babu wani wanda ya ke amsawa sai Ali (a.s) daga nan sai Manzon Allah ya yarda ya kana kuma ya bukaci wadanda suke gurin da su yi masa da'a da biyayya don shi ne zai kasance dan'uwansa, wasiyyinsa, mataimakinsa kana kuma halifansa a bayansa. DA'AWAR SARARI To da yake dai an saukar da sakon Musulunci ne ga dukkan duniya ba wai kawai ga wasu mutane na daban ba, don haka babu makawa Manzon Allah ya isar da wannan sako ga kowa da kowa, to amma ta yaya? Sannan kuma dole ne ya jira umarni daga Ubangijinsa. Wannan umarni kuwa ya zo ne a lokacin da Allah Ya saukar da wannan aya: Ka tsage gaskiyar abin da aka umurce ka da shi, kuma ka yi watsi da kafirai. (Surar Hijr:94) Bayan saukar wannan aya, sai Manzo (s.a.w.a) ya tafi ya hau dutsen Safa da ke Makka, ya tara mutane a wajen, sannan ya bayyana kiransa na Allah ga mutane. Duk da cewa mafi yawan mutane sun gujewa sakon nasa, sai dai wasu sun amsa sun bayar da gaskiya. Haka nan labarin kiran Allah ya shiga kowane gida. Daga mutanen da suka ba da gaskiyar har da dangin Annabi (s) irinsu Ja'afar bn Abi Talib, Ubaidah bn Harith da dai sauransu. Amma irin wannan ci gaba da Musuluncin ke samu ya sanya mushirikan Makka cikin matukar bakin ciki, saboda tsoron kubucewar mulkinsu, don haka sai suka dauki matakan gallazawa duk wanda ya karbi wannan addini, ba don komai ba sai don rashin wata hujja da za su kare bautar gunki ko kuma hana mutane karbar Musulunci. Daga cikin irin mutanen da aka gallazawa akwai Bilal al-Habashi, Suhaib, Ammar bn Yasir da mahaifansa Yasir da Sumayya da dai sauransu. Kafin dai a kai ga gallazawan, kafiran Makkan sun yi kokarin raba al'umma din da Manzon Allah (s) ta hanya nuna musu cewa shi makaryaci, mawaki, mai sihiri da mahaukaci; suka shiga yi masa izgili. Sai dai wannan bai raunana Manzon Allah (s.a.w.a) ya hana shi ci-gaba da kira zuwa ga gaskiya ba; don haka sai suka dauki matakin jawo hankalin shi ta hanyar bijiro masa abubuwan jan-hankali da hure kunne, na daga mulki, shugabanci da dukiya. Sai dai Manzo (s.a.w.a) ya ki amsar duk wananna yana mai ci gaba da abin da ya sa a gaba; don haka sai suka dauki matakin kuntata masa da iyalinsa da dukkan wadanda suka yi imani da shi, sai dai kuma a nan ma dai kokarinsu ya tafi a banza a sakamakon gwarzantakar Manzo da tsayuwarsa bisa gaskiya tare da kariyar Abu Talib, matarsa Khadija da kuma Aliyu bn Abi Talib gare shi. Har ma an ruwaito shi yana cewa wannan addini na Musulunci ya tsaya da kafarsa ne saboda kariya irinta Abu Talib, dukiyar Khadijah da kuma takobin Ali (a.s).  

____________ (1)- Ibin Athir, cikin al-Kamil, juzu'i na 2, shafi na 24; da Biharul-Anwar, juzu'i na 18, shafi na 164; da Fiqihul-Sirah, na Sheikh Muhammad Gazzali, shafi na 102.      

Abubuwan Da Suka Faru A Makka

HIJIRA ZUWA HABASHA Bayan da Manzon Allah (s) ya fito fili da wannan kira nasa da kuma irin karbar da al'umma suka yi wa kiran, sai kafiran Makka suka fara tunanin hanyoyin da za su bi wajen kawo karshen wannan barazana da take fuskantarsu. Don haka sai suka fito wa lamarin ta hanyoyi daban-daban, daga cikin hanyoyin kuwa har takurawa al'ummar musulmin da kuma azabtar da su. sai Manzo (s.a.w.a) ya ga cewa bari ya yi wa wani adadi daga mabiyansa izini da yin hijira zuwa Habasha, don ya samar musu kariya da matsera daga takurawa. Don haka sai mazaje goma sha daya da mata hudu suka yi hijirar, suka saura a Habasha har na tsawon watanni uku, har zuwa lokacin da labari ya isa gare su cewa Kuraishawa sun mika kai. Wannan ya sa suka dawo Makka, sai dai sun sami cewa Kuraishawa na nan da halinsu ba su canza ba, wato dai suna ci gaba da cutar da Musulmi da azabtar da su. Sai Manzo (s.a.w.a) ya hore su da sake yin hijira zuwa Habasha. A wannan karon adadinsu ya kai maza tamanin mata goma karkashin ja-gorancin Ja'afar dan Abi Dalib. Kuraishawa dai sun yi matukar tsorata da wannan hijira, don haka sai suka yi kokarin dawo da su, in ban da cewa sarkin Habasha Najjashi, wanda ke bin addinin Annabi Isa (a.s) a wannan lokacin, ya ki yarda da bukatun 'yan aiken Kuraishawa, wato Amr bin As da Ammara bin Walid. 'Yan aiken na Kuraishawa sun yi kokarin shafa wa musulmin bakin fenti a wajen sarkin Habasha don ya ki karbar masu hijirar; bugu da kari kuma suna dauke da kyautuka masu yawa daga Kuraishawan zuwa gare shi; sai dai kuma jawabin da Ja'afar dan Abi Dalib ya yi a gaban sarkin ya bata musu shiri da kuma sanya sarkin ya ki amincewa da bukatan 'yan aiken, inda ya ke cewa: Ya kai wannan sarki, hakika mun kasance mutanen jahiliyya Muna bautar gumaka, muna cin mushe, muna aikata alfasha, ba ma sadar da zumunci, muna munana makotaka, mai karfi a cikinmu na danne mai rauni. Haka muka kasance har Allah Ya aiko da Manzo zuwa gare mu, wanda mun san danganensa da gaskiyarsa, rikon amanarsa da kamun kan sa; sai ya kira mu zuwa ga Allah don mu kadaita Shi kuma mu bauta mi Shi, mu kuma janye daga abubuwan da muka kasance, mu da iyayenmu, muna bauta musu na daga duwatsu da gumaka. Ya hore mu da fadar gaskiya, rokon amana, sadar da zumunci, kyautata makotaka da kamewa daga da abubuwan da aka haramta da zubar da jinni. Ya kuma hana mu aikata alfasha, shedar zur, cin dukiyar maraya da yin kazafi. Haka ya hore mu da bautar Allah Shi kadai ba tare da mun hada Shi da komai ba. Ya hore mu da yin salla da zakka da azumi. Sai Najjashi ya ce masa: "Ko kana a tare da kai akwai wani abu daga abin da Manzo Muhammadu ya zo da shi daga Allah?". Sai Ja'afar ya ce na'am. Sai ya karanta masa wani sashi na Surar Maryam. Jin wannan aya, sai Najashi da wadanda suke tare da shi na daga malaman Kirista suka fashe da kuka. Sai Najashi ya ce: " Hakika da wannan da abin da Isa ya zo da shi sun fito ne daga tushe guda." SANYA TAKUNKUMI GA MUSULMI Lalacewan shirin Kuraishawa na kawo cikas ga hijira zuwa Habasha ya kara kaimin adawarsu da da'awar Musulunci, don haka sai suka kuduri aniyar lankayawa Bani Hashim takunkumin cinikayya, cudanya da auratayya; sai suka rubuta haka a wata takarda wadda mutane arba'in daga shugabannin Kuraishawa suka rattabawa hannu a kai. Sai suka kange Banu Hashim a Shi'ibi Abi Dalib, suka zama ba sa fita daga wannan guri sai a lokutan Ummura a watan Rajab, da lokacin aikin Haji a watan Zul-hijja saboda girman matsayin a tsakaninsu da sauran Kuraishawa. Musulmi sun shiga wani mawuyacin hali matuka, saboda hatta abincin da zai ishe su ba su da shi, kunci ya kai musu ko'ina. Haka wannan takunkumi ya ci gaba har tsawon shekaru uku, lokacin da takunkumin ya kawo kare yayin da Allah Ya turo sari ya cinye wannan takarda da aka sanyawa hannu, bai bar kome ba sai kalmar Bismikal-Lahumma (wato da SunanKa ya Allah), dake rubuce a saman ta. Wannan al'amari ya yi matukar ruda mushrikai, ya kuma sa musu karin dalili a kan gaskiyar da'awar Manzo (s.a.w.a). SHEKARAR BAKIN CIKI Duk da cewa takunkumi ya kare, sai dai haka bai zama karshen matsaloli ba; domin Khadija bint Khuwailid, matar Annabi (s.a.w.a) kuma babbar uwar muminai, wadda ta kasance farkon wadda ta bada gaskiya da shi ta kuma gaskata shi, ta kuma yi tarayya da shi cikin wahalhalun isar da sako; ta bayar da dukiyarta saboda Allah. Rasuwarta ta kasance kafin hijira (zuwa Madina) da shekaru uku, kuma a watan Ramalana mai alfarma. Manzo (s.a.w.a) ya ji wannan mutuwa kuma ya yi bakin ciki matuka. Bayan wafatin Khadija (RA) da kwanaki uku kuma sai Abu Dalib, mai kariya ga Annabi kuma madogaran sakonsa, shi ma ya rasu. Labarin rasuwar wannan baffa na shi ya sa shi cikin karin bakin ciki, yayin da ya je wajen gawarsa, ya shafi gefen goshinsa na dama da na hagu, sannan ya ce: Ya baffa, ka reni yaro, ka rike maraya kuma ka yi taimako mai girma, Allah Ya saka maka da alheri a kan abin da ka yi min. Saboda tsananin tasirin wadannan abubuwa biyu a ci-gaban yunkurin tarihin Musulunci ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya sa wa wannan shekara suna Shekarar Bakin Ciki. TAFIYA ZUWA DA'IFA Saboda kunci da damuwar rashin Matarsa da Baffansa, kana kuma ga sabuwar gaba da kafiran Makka suka dasa saboda karfin gwuiwan da suka samu saboda rasuwar Abu Talib, Manzon Allah (s) ya kuduri aniyar zuwa garin Da'ifa don isar da sakon Musulunci; amma abin takaici mutanen Da'ifan ba su karbi wannan sako ba. Babu wanda ya amsa wannan kira na Manzon Allah (s) in ban da wani tsohon mabiyin addinin Kirista manomi wanda ake kira da Adhasu, shi ne kawai ya karbi Musulunci. Larabawan Da'ifa, maimakon karbar sakon Musulunci, sai suka umarci 'yan iskan gari da kananan yara da su jefi Manzon Allah (s) da duwatsu duk inda ya tafi. Ko da Manzon Allah (s) ya ga wannan sako nasa ba zai yi wani tasiri ga wadannan mutane na Da'ifa masu kekasassun zukata ba, sai ya koma garin haihuwarsa wato Makka. GANAWA DA WAKILAN MUTANEN MADINA Bayan dawowa ma dai Manzon Allah (s) ya ci gaba da kiran mutane da kuma kabilu daban-daban zuwa ga Musulunci, sai dai kuma a wannan karon ma dai ba a samu wasu adadi mai yawa da suka karbi wannan da'awa ba. A shekara ta goma sha daya bayan aiko Annabi ne, a lokacin da ya rika bijiro da kiransa a lokutan aikin haji ne ya hadu da wasu mutane daga Khazraj, wadda daya ce daga manyan kabilun nan biyu na Yathrib (wanda ya zama Madina bayan hijira); wadannan mutane ne kuwa suna karkashin jagorancin As'ad bn Zurar, inda ya bijiro musu da Musulunci su kuma suka amsa masa. Wannan tawaga ta yi matukar farin ciki da wannan kira da kuma imanin da suka yi da shi. Daga nan sai wannan shugaba na su ya bukaci Manzon Allah (s) da ya hada su da wani daga cikin sahabbansa don su tafi Yathrib din don ci gaba da isar da sakon Musulunci da kuma karantar da wadanda suka amshi kiran. Hakan kuwa aka yi, sai suka koma Yathrib suna kiran mutane zuwa ga Musulunci. Komawarsu ke da wuya sai suka fara wannan da'awa da kuma kiran jama'a zuwa ga wannan sabon addini kana kuma hanyar tsira duniya da lahira da dukkanin al'umman duniya, amma fa ga wanda ya yi imani da shi. Lalle cikin dan lokaci kadan an samu nasarori kala-kala inda aka samu mutane masu yawan gaske da suka Musulunta. MUBAYA'AR FARKO A AKABA Bayan haka, a shekarar da biyo baya, sai wasu mutum goma sha biyu daga mutanen Yathrib suka je wajen Manzo (s.a.w.a) a Akabah, suka yi mishi mubaya'a a kan cewa: "ba za su hada komai da Allah ba, ba za su yi zina ba, ba za su kashe 'ya'yansu ba, ba za su yi zaluncin da suka kirkira da hannunsu da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba masa a kan wani abu mai kyau ba; in har sun cika alkawarin to suna da Aljanna; in kuwa suka tauye wani abu daga wannan, to al'amarinsu na wajen Allah, in ya so ya azabtar da su, in ya so ya yi musu afuwa." A lokacin aikin hajin da ya biyo bayan wannan, wato a shekara ta goma sha uku da aiko shi, sai wata babbar tawaga daga Yathrib ta yi wani taron asiri da Manzo (s.a.w.a) a Akabah; tawagar ta kunshi maza saba'in da mata biyu. Wannan ne ya samar da wani yanayi da da'awar Musulunci za ta tsayu a kan ta wajen isar da babban sako. Sai Manzo (s.a.w.a) ya hori muminai da yin hijira zuwa Yathrib. Sai Musulmi suka yi ta kwarara, a boye cikin duhu, zuwa gidan imani, suna masu barin dukiyoyinsu da gidajensu saboda addinin Allah Madaukaki.

 Hijirar Manzon Allah (s) Daga Makka Zuwa Madina

BABBAR HIJIRA DAGA MAKKA ZUWA MADINA:

Saboda ganin irin tasirin da Musulunci ke samu da kuma gazawarsu wajen dakushe haskensa, kafiran Makka sun shirya makirci na kokarin kashe Manzon ALlah (s). Bugu da kari kuma rasuwar Abu Talib, garkuwan nan na wannan jaririn addini, ya dauke wannan babban abin da ke kare su daga kashe Manzon (s). To sai dai kuma kafiran Makkan kulle-kullensu ba tare da la'akari da cewa Ubangiji Allah Yana sane da abin da suke kullawa ba. Don haka Allah Madaukakin Ya aiko da Mala'ika Jibrilu (a.s) da ya sanar da Annabin wannan mummunan kulli na kafiran, sannan kuma ya bukaci Manzon naSa da ya yi hijira ya bar Makkan zuwa Madina. Wannan umarni dai na Ubangiji ya biyo bayan taron da Kuraishawa suka yi a wajen taronsu na Darul-Nudwah, inda suka dace a kan kashe Annabi (s.a.w.a) ta hannun wasu gungu na 'yan iskan gari da ya kunshi mutum guda daga kowane babban gida daga gidajen Kuraishawa, don jinin shi ya tafi a banza; wato ya bace a tsakanin kabilu ta yadda babu wanda za a dorawa alhakin haka. Sai Kuraishawa suka yi kokarin gaggauta aiwatar da abin da suka dace a kai da daddare, sai dai Abu Lahab ya ba su shawarar aiwatar da wannan barna da sanyin safiya; don haka sai suka sa gidan Annabi karkashin matsanancin sa-ido don kar al'amari ya kufce daga hannunsu. Don haka da wannan dare ya yi sai wadannan 'yan iskan gari suka taru suka kewaye gidan Manzon Allah (s) da nufin aikata abin da suke son aikatawa da asuba. To a daidai wannan lokaci sai Allah Ya umarci Annabi (s) da ya fice daga gidan ya kama hanyar Madina, Ya kuma umarce shi da ya umarci Aliyu bn Abi Talib (a.s) da ya kwanta a kan gadonsa. Daga nan sai Manzon Allah Ya gaya wa Ali wannan umarni, sai Ali ya ce masa, shin za ka tsira idan na kwanta din, Manzo ya ce masa na'am, jin haka nan take sai ya kwanta a kan gadon ya rufu da mayafinsa, shi kuma Manzo ya ratsa tsakanin kafiran wadanda suke barci ya fita yana karanta fadar Allah: Muka kuma sanya wani shamaki a gabansu da wani shamaki a bayansu, sai muka lullubesu alhali ba sa gani. (Surar Yasin:9) Daga nan sai Manzon Allah (s) ya fita ya je ya samu daya daga cikin sahabbansa, wato tsohon abokinsa Abubakar bn Abi Kahafa, wanda saboda wasu dalilai ya ga bai dace ya bar shi a garin Makkan ba, don haka ya je ya same shi suka wuce, shi kuwa Imam Ali (a.s) ya ci gaba da kwanciyarsa cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tsoro ko fargaba. Su kuwa kafiran suka ci gaba da kewaye gidan a wasu lokuta suna lekowa cikin ganin Annabin don su ga ko yana nan, inda suka ganin Imam Ali a kwance amma suna zaton Manzon Allah ne. Daga karshe dai kafin wayewar gari wannan kungiya ta 'yan iska ta fada gidan Annabi (s) cike da amincewa da gudanar da wannan mummunan aiki. Amma duk da haka tsayuwa da suka yi cikin dare ya zama aikin banza, don kuwa wanda suke nema din ya riga da ya fita ya tafi, wanda suka gani ya fito daga cikin mayafi shi ne Zakin Allah Ali (a.s). Nan take cikin kunya da tsoro sai wadannan kafirai suka tambayi Imam Ali (a.s) ina Muhammadu ya ke, cikin kakkausar murya sai ya amsa musu da cewa: "Hala kun ba ni ajiyarsa ne?". Ganin haka sai suka fita cikin kunya suka koma inda suka fito. Ta haka ne Allah Madaukakin Sarki ya kubutar da ManzonSa daga makircin mushirikai, kana kuma Ya fitar da shi cikin aminci daga cikin wadannan kafirai masu makauniya zuciya kuma ba tare da sun ganshi ba. Wannan lamari na kwanciyar Imam Ali (a.s) a kan gadon Manzo da kuma tsirar da Manzon ya yi a sanadiyyar haka dai yana da wani muhimmanci, domin ya bayyanar da irin matsayin Imam Alin da kuma irin tsananin sadaukarwarsa don kare tafarkin Musulunci da kuma rayuwar dan'uwansa Manzon Allah (s). Don kuwa Ali (a.s) ba tare da tsoro ba ya yarda ya kwanta a gadon Annabi, ya yarda ya sanya rayuwarsa cikin hatsari don Annabi ya tsira da ransa. Hakika idan har rayuwar Abu Talib (a.s) ta kasance garkuwa a kan kafiran Makka daga cutar da Annabi a wancan lokacin, to yanzu da ba ya nan ga jarumin dansa nan Ali ya cike wannan gurbi. A halin yanzu ga shi ya sadaukar da ransa don Annabi (s) ya rayu. Saboda irin wannan sadaukarwa da Imam Ali (a.s) ya yi ne ma Allah Ya saukar da aya, wadda take cewa: Kuma daga mutane akwai wadanda ke sayar da kansa don neman yardar Allah, Allah kuwa Mai tausayi ne ga bayi (Surar Bakara:20) Daga karshe dai Allah ya kawo karshen wannan makirci da kuma wadannan makirai, don kafin su ankara Annabi da abokin nasa sun fice daga Makka sun kama hanyar Madina. To amma don gudun kada kafiran su biyo su, sai suka buya a cikin wani kogo da ke kimanin mil uku daga kudancin garin Makka, wanda ake kira da kogon Thaur. Hakan kuwa aka yi don kuraishawa cikin gaggawa sun fito neman inda Annabin ya ke, inda suka iso har bakin wannan kogo, amma dai sai Allah Ya nufi wani gizo-gizo da ya yi saka a wajen, sannan ga wata tsuntsuwa kuma tana kwanci a bakin kogon ta yadda ba za a iya fahimtar akwai wani mutum a cikin kogon ba, don ba yadda za a yi mutum ya shiga cikin wannan kogo ba tare da kori wannan tsuntsuwa da kuma yaye wannan saka na gizo-gizo. To amma dai lokacin da suka iso wannan kogo dai, hankalin Abubakar ya tashi saboda tunanin abin da zai iya samunsu, har ma ya fara kuka, to amma sai Allah Ya saukar masa da nitsuwa a zuciyarsa don kada ya yi sanadiyyar kafiran su gano su, wanda hakan zai sa duk wannan kokari da aka yi a baya ya zamanto aikin baban giwa. Lokacin da kafiran suka sami tabbas din cewa babu kowa cikin wannan kogo, sai suka juya cikin yanke kaunar samun Manzon Allah (s). Ta haka ne Manzon Allah da abokin nasa suka fito suka kama hanyar Madina Bayan tafiya na 'yan kwanaki, Manzon Allah (s) ya isa wani waje dake wajen Madina da ake kira Kubah, inda ya ya da zango yana jiran isowar Ali bin Abi Dalib (a.s) da ayarin Fatimomin bani Hashim, wato Fatima mahaifiyarsa (Ali), Fatima 'yar Annabi, Fatima 'yar Zubairu bin Abdul-Mudallibi da Fatima 'yar Hamza. Lokacin da Ali (a.s) ya iso Kubah sai Manzo (s.a.w.a) ya tarbe shi, ya rungumi shi, har sai da hawaye suka zubo masa saboda tausayawa wahalhalun da ya sha akan hanya. Bayan isowar Imam Ali (a.s) Manzo ya saura a Kubah har na tsawon kwanaki biyu, a lokacin ne ma ya gina Masallacin Kubah bisa shawarar Ammar bin Yasir. Wannan ne masallacin farko a Musulunci. Daga nan sai Manzo ya hau abin hawan shi ya nufi Madina. Tarbar da aka yiwa Annabi dai lokacin da ya isa Madina ta kasance ta gama-gari ce. Dama mutane na jiran isowarsa. Lokacin da ya shiga garin sai mutane suka yi masa dandazo da ba a taba ganin irinsa ba. Mutane na rige-rigen haduwa da shi. Ya kasance ba ya wuce wani gida har sai mutanen gidan sun gayyace shi da ya shigo, sai dai shi ya kasance yana ce musu: "Ku ba taguwar hanya, domin hakika ita wadda aka yi wa horo ce". Daga wannan hijira zuwa Madina ne aka fara kidayar kalandar Musulunci, wadda kuma malamai suka ce an yi ne ranar daya ga watan Rabi'ul Awwal.  

Takaitaccen Bayani Kan Madina

Garin Yathrib (ko kuma Madina) gari ne da ke tsakiyar sahara da ake da koramai da rijiyoyi masu yawa, bishiyoyin dabino da sauran itatuwan marmari kuma sun kewaye garin. Yana kimanin kilomita 450 daga arewacin garin Makka. Kabilun larabawa nan masu bautar gumaka, wato Aus da Khazraj, su suka mamaye garin. Haka kuma akwai wsu kabilun Yahudawa kamar su Bani Kuraiza, Bani Mugir da Bani Kainuka da suka yo hijira zuwa garin Madina don jiran Annabin karshe da zai zo kamar yadda suka karanta a cikin tsoffin littattafansu. Amma akwai mummunar gaba tsakanin wadannan kabilu biyu masu bautar gumaka (Aus da Khazraj), wanda hakan ya haifar da yakoki da lalata dukiyar juna a tsakaninsu. Bugu da kari kuma babu jituwa tsakanin wadannan larabawa da wadancan yahudawa: domin su Yahudawan na amfani da littafansu suna yin izgili ga wadannan masu bautar gumaka na cewa da sannu wani Annabin Allah zai bayyana a cikin Larabawa kana kuma ya zo garin Madinan, kuma zai kawo karshen wannan mummunar hanya tasu. Amma abin mamaki lokacin da Manzon Allah (s) ya bayyanar da annabcinsa kuma ya yi hijira zuwa garin Madina, wadannan kabilu na Larabawa, wato Aus da Khazraj, su ne suka bar bautar gumaka suka karbi Musulunci, amma wadancan Yahudawan da kakanninsu suka yi yo hijira saboda jiran Manzon Allah (s), sun ki karbar wannan sako na Musulunci. Dalilinsu dai shi ne shi Manzon Allah (s) balarabe ne da ya fito daga tsatson babban dan Annabi Ibrahim (a.s), wato Annabi Isma'il (a.s), don haka bai zama karbabbe ba a wajen yahudawa. A wani bangaren kuma wannan hijira ta Manzon Allah (s) zuwa gari Madina ta sa kabilun Aus da Khazraj sun tuna da abubuwan da Yahudawan nan kr fada masu dangane da Annabi (s), don haka cikin gaggawa suka karbi sakon Musulunci, wanda hakan ya kawo karshen mummunar gabar da ke tsakaninsu. Allah Madaukakin Sarki Ya cika zukatansu da kaunar juna wadda a da ba su taba samun irinta ba, Ya kuma hada su karkashin tutar Musulunci mai girma. Amma su wadancan yahudaw, cikin tsananin gaba,sai suka juya wa Manzon Allah (s) baya kamar yadda suka yi wa Annabi Isa (a.s) a karnoni shida da suka wuce.

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Madina

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Madina Hijirar Manzon Allah (s) zuwa garin Madina ya bude wani sabon shafi na wannan sako na Allah, don a lokacin ne Musulunci ya fara kafuwa har ya zama ya fara yaduwa zuwa kowane bangare na kasashen Larabawa saboda samun karuwar musulmi da aka yi. A baya dai mun nuna cewa Manzon Allah (s) yana da shekaru hamsin da uku a lokacin da ya yi wannan hijira; don haka ya zauna a garin Madina ne na tsawon shekaru goma, inda a garin ne ya kare sauran rayuwarsa da ke cike da abubuwan mamaki; don kuwa a cikin wannan lokaci ne wannan sako na Ubangiji ya kai wani matsayin na cika, kuma muhimman abubuwa suka yi ta faruwa inda daga karshe dai suka haifar da kakkarfar hanya ta yaduwar Musulunci da kuma isarsa ko ina a duniya. Don haka a nan za mu yi dubi ne cikin manyan abubuwan da suka faru dangane da rayuwar Annabi Muhammad (s) da Musulunci a garin Madinan:   GINA MASALLACI NA FARKO   Da shiga garin Madina dai abu na farko da Annabi (s) ya yi shi ne gina masallaci, wato masallacin farko a tarihin Musulunci. Ginin wannan masallaci na daga cikin muhimman ci gaba ga musulmi wadanda yanzu suka sami matattara ta kansu inda za su rika taruwa, makaranta inda za su rika koyon karatun Alkur'ani, kana kuam cibiyar karbar umarni da hani daga shugabansu. A halin yanzu lokacin buya don tsoron cutarwa ya wuce. A wannan lokacin dai dukkan al'ummar musulmi da suka hada da Muhajirai (Mutanen Makka da suka yi hijira) da kuma Ansar (mutanen Madina da suka tarbe su) ne suka ba da himma da dukkan karfinsu wajen gina wannan masallaci, wanda daga baya ake kiransa da Masjidun Nabi (Masallacin Annabi). An gina wannan masallaci ne da yumbu da takkan dabino don yi masa rufi. Manzon Allah (s) da kansa ya kasance cikin masu ginin wannan masallaci, inda da shekara ta zagayo ya fadada masallacin saboda karuwar da musulmi suke yi. Bayan gina wannan masallaci dukkan musulmi cikin farin ciki sukan taru don gudanar da salloli a cikinsa karkashin jagoranci Manzon Allah (s). Bayan salla kuma ya kan gabatar da huduba, ya koyar da musulmi Alkur'ani da dokokin Musulunci; haka kuma ya kan tattauna da su, ya kan saurari matsalolinsu don samun hanyoyin da za a magance su da dai sauransu. Don haka dai wannan masallaci ya zama helkwatar gwamnatin Musulunci ta farko wadda Manzon Allah (s) ya kafa. Har yanzu wannan masallaci na nan, ko da yake an kara fadada shi da kuma kawata shi cikin karnonin da suka wuce. A halin yanzu kuma kabarin Manzon Allah (s) a cikin wannan masallaci ya ke, inda miliyoyin musulmi daga ko ina kan kai masa ziyara kowace shekara.   KULLA 'YAN'UWANTAKA TSAKANIN MUSULMI   Abu na biyu mai matukar muhimmanci da Manzon Allah (s) ya yi bayan isarsa Madina shi ne hada 'yan'uwantaka tsakanin Muhajirai da Ansar, inda ya hada kowani Muhajiri da Ansar guda a matsayin dan'uwa. Mai son karin bayani kan wannan kulla 'yan'uwantaka sai ya matsa nan Kulla 'Yan'uwantaka don ganin karin bayani.   MAKIRCIN KURAISHAWA BAYAN HIJIRA   Kubutar Manzo (s.a.w.a) daga hannun Kuraishawa da isarsa Madina lami lafiya sun kara tunzura Kuraishawa da sa su ci-gaba da makirce-makircensu da shirye-shiryensu na gamawa da shi. Wannan bai kasance wani boyayyen abu ba, maimakon haka shugabannin Kuraishawa sun sha fitowa fili su bayyana haka. Kuraishawa sun ci-gaba da yi wa Musulmi bita-da-kulli na kuntatawa da cutarwa, sawa'un Muhajirai ne ko duk wanda suka san musuluntarsa a Makka. Haka sun rikewa Musulmi dukiyoyinsu da mamaye gidajensu da sauran kayayyakinsu da ke Makka. Ta wata fuska kuma, sun kasance suna bin diddigin irin yanayin da Manzo (s.a.w.a) ke ciki, suna kwadaitar da wannan kabila ko waccan da cin zarafin Annabi da mabiyan shi. Wannan ya sa Manzon Allah daukan wasu matakai don samar da kariya ga da'awa da kiyaye shi. Farkon matakin da Annabi (s.a.w.a) ya dauka shi ne kyautata yanayin da ke kewaye da Madina, inda ya aika da wasu tawagu, ya ja-goranci wasu zuwa kabilun da Mishrikai da ke makwabtaka da su. Wannan ya haifar da wasu yarjeniyoyin sulhu da hadin gwuiwa tare da su, don gujewa yaki da zubar da jini. A daidai lokacin kuma, Manzo (s.a.w.a) ya kasance yana daidaita yanayi a cikin Madina, yana kunce makirce makircen kafiran Kuraishawa na zaburar da mazauna wannan yanki a kan yaki da musulmi. A wani bangaren kuma shi da kansa Manzo din (s) ya kan dauki wasu matakai na takurawa wa wadannan kafirai da kuma sanya musu takunkumi, ganin cewa su ma kafiran sun fara kwace dukiyoyin al'umman musulmi, duk wadannan matakai dai da Annabin ya dauka da nufin yin maganin kulle-kullen da kafiran suke yi na kai wa musulmi hari. Lalle babu shakka dai irin wadannan matakai na Annabin (s) ya dauka sun yi nasara bugu da kari kuma kan cewa wadannan kabilu da suka kulla yarjejeniya da musulmi su ma sun cika alkawurran da suka yi. Don haka sai kafiran suka fara tunanin fada wa musulmin da yaki don gamawa da su. Don haka ne ma ake cewa dukkan yakukuwan da Manzo (s) ya yi su ne a matsayin kariyar kai ba wai don tsokana ba, kamar yadda haka ke bayyane ga wanda ya karanta yanayoyinsu kamar yadda ya kamata. A kan haka Allah Madaukaki ke cewa: An yi izini (na yin yaki) ga wadanda ake yakarsu, do an zalunce su, hakika kuma Allah Mai iko ne bisa taimakon su. (Su ne) Wadanda aka fitar daga gidajensu ba da wani laifi ba, sai don kawai sun ce: 'Ubangijinmu (shi ne) Allah'. Surar Hajji:39-40.   YAKUKUWAN MANZON ALLA (S) NA KARE KAI:   Ana iya ganin karin bayani ta nan:   KARSHEN MAKIRCE-MAKIRCEN YAHUDAWA Hakika tun lokacin da Manzon Allah (s) ya koma garin Madina, sai wadannan miyagun Yahudawa na Madina suka bijire masa da kiransa na Musulunci, kamar yadda suka nuna gaba da kiyayya ga Annabi Isa (a.s) a shekaru masu yawa da suka wuce. Wadannan makiran Yahudawa sun hada kai da mushrikan Makka don kawo karshen Musulunci; don haka ne ma suka kulla makircin kashe Manzo (s), duk kuwa da yana kyautatawa da taimakonsu don kwadaitar da su ko za su karbi wannan sako na Musulunci. Amma ko da ya ga makirce-makirce da zaluncinsu sai ci gaba suke yi, sai ya ga ba shi da zabi face ya yake su don kare Musulunci da musulmi. Ya yi fito na fito ne da su ne a yakin nan da ake kira Yakin Khaibara, wanda bayani kansa ya wuce. A yayin wannan yaki dai Imam Ali (a.s) ya nuna jarunta kwarai da gaske, inda daga karshe dai Annabi (s) ya yi nasara akan wadannan yahudawa kuma aka kawo karshen katsalandan dinsu.   SULHUN HUDAIBIYYA   Wani muhimmin al'amari da ya faru a rayuwar Manzon Allah (s) da ci gaban sakon Musulunci shi ne Sulhun Hudaibiyya. Abin da ya faru dai shi ne: Wata rana Manzon Allah (s) ya yi mafarkin cewa shi da sahabbansa sun shiga Dakin Ka'aba a garin Makka don yin dawafi, amma kafiran Makkan suna kokarin hana su. Saboda wannan mafarki ne sai Manzo (s) ya yanke cewa zai tafi Makka shi da sauran musulmi kimanin dubu daya da dari biyar don yin aikin hajji, hakan kuwa ya faru ne a shekara ta shiga bayan hijira. A lokacin da suka wani wuri da ake kira Hudaibiyya, sai suka tarar da kafirai sun toshe duk wata hanyar shiga Makka; ganin haka sai Annabi (s) ya aike da wani manzo nasa zuwa ga kafiran don shaida musu manufar zuwansa da kuma nuna musu a shirye yake ya yi sulhu da su. Dama Kuraishawa na fama da zafin galabarsu da aka yi a yakin Khandak; don haka da suka lura da irin karfin Manzo (s.a.w.a) da nacewarsa a kan abin da ya ke so, suka kuma riski irin raunin da suke fama da shi da gazawarsu a yaki, sai suka amsa kiran Manzo (s.a.w.a). Da haka aka rattaba hannu a kan yarjejeniyar sulhu. Daga cikin yarjejeniyar da aka kulla har da cewa tawagar musulmi a wannan shekarar ba za ta shiga Makkan ba, maimakon haka sai ta koma shekara ta gaba da dai sauran sharuddan da aka cimma. Saboda hakan ne sai Manzon Allah (s) da sahabbansa suka koma Madina, amma da shekara ta zagayo, sai suka dawo inda suka shiga Makkan kuma suka gudanar da wannan ibada da suke son gabatarwa. Ta haka ne dai mafarkin da Annabi(s) ya yi ya tabbata. Wannan sulhu da aka cimma dai ya haifar da babban tasiri a tarihin ci-gaban Musulunci, yayin da ya bayar da dama ga Musulmi wajen isar da sakonsu ga wadanda ba Kuraishawa ba na daga mazauna tsibirin Larabawa, sannan suka sami sararin sabuwar gwamnatinsu da karfafa ta.   KIRAN SHUWAGABANNI ZUWA GA MUSULUNCI   Cin garin Makka da yaki da rugurguza gumaka daga Dakin Ka'aba da musulmi suka yi ba karamar nasara ba ce gare su (musulmi); don haka da kuma irin halayen kwarai da dattaku da Manzon Allah (s) ya nuna wa makiyansa bayan ya samu nasara akansu, alhali kuwa suna tunanin zai musguna musu da kuma neman daukan fansa kan abubuwan da suka masa, ya sa da dama daga cikinsu suka karbi Musulunci. Wannan nasara dai da musulmin suka sam ya sa a halin yanzu sun kasance masu karfi, to ganin haka da kuma cewa hasken Musulunci ya kori duhun zalunci da kafirci daga mafi yawa daga cikin daular larabawa, sai Manzon Allah (s) ya ga cewa a halin yanzu ya zama wajibi a sanar da sauran daulolin duniya makwabta wannan sako na Musulunci da kuma kiransu zuwa gare shi. Don haka sai ya aika da wasiku zuwa ga sarakunan kasashen Farisa, Rum, Habasha da sauran sarakunan kasashe da kabilu don kiransu zuwa ga shiriya da hasken Musulunci. Koda wakilan Manzo din (s) suka isa, wasu sarakunan sun karbi Musulunci, wasu kuma sun ki amincewa amma sun yarda a yi sulhu, yayin da wasu kuma irin su sarkin Farisa, wadanda ba wai kawai sun ki amincewa da sakon ba ne, a'a har ma ya ga wasikar Manzon (s) suka yi da kuma wulakanta wakilin da ya kai musu sakon.   MUBAHALA DA KIRISTOCI   Daga cikin wasikun da Annabi (s) ya aika wa sarakuna da shugabannin kasashen don kiransu zuwa ga Musulunci har da wanda ya aika wa Kiristocin Najran da Yaman. Lokacin da suka karbi wasikarsu, wadannan ba wai kawai ma sun ki yarda da Musuluncin ba ne face ma dai sai suka yi aniyar zuwa garin Madina don kalubalantar Annabi (s) da kuma kokarin kare mummunan akidar nan tasu ta cewa Annabi Isa dan Allah ne kuma an giciye shi. Koda isowarsu garin Madina sai Manzon Allah (s) ya gabatar musu da dalilai masu karfi daga Littafan Ubangiji da suka gabata dangane da gaskiyar Musulunci, to amma duk da haka dai sun ki yin imani. Don haka sai bangarorin biyu suka yanke shawarar haduwa a wani budadden don yi la'anceceniya da kuma rokon Allah Ya saukar da azaba akan makaryaci. Don haka sai Allah Madaukakin Sarki ya umarci ManzonSa (s) da ya tafi da danginsa makusanta wannan wuri na la'anceceniya (Mubahala), Allah Yana cewa: Sannan wanda ya yi jayayya da kai game da shi, bayan abin da ya zo maka na ilmi, to ka ce: Ku zo mu kira 'ya'yanmu da 'ya'yanku, da matanmu da matanku, da mu kanmu da ku kanku, sannan mu shiga yin addu'a don sanya tsinuwar Allah a kan makaryata (Surar Ali Imrana: 3:16) Ko da lokacin ya yi, sai shugabannin wadannan kiristoci suka zo wannan wuri da jama'arsu, kana shi kuma Manzon Allah (s), a bisa umarnin Allah, sai ya zo danginsa makusanta, wato: 'Yarsa Fatima (a.s) a gaba, yana rike da jikansa Hasan a hagu, Husaini kuma a dama sannan sirikinsa kuma dan baffansa Aliyu bn Abi Talib (a.s) yana biye a baya, ya shigo wannan fili. Hakika wadannan kiristoci dai ba su taba ganin mutane masu kwarjini irin wadannan makusantan Annabi ba. Don haka ko da shugabansu ya ga Manzo da wadannan taurari iyalai na sa, sai ya razana, ya gano cewa wallahi ba su da gaskiya kuma idan har suka bari aka yi la'anceceniya to lalle fa Allah zai la'ancesu saboda wadannan mutane. Don haka sai ya janyo mutanensa ya gaya musu cewa wallahi ya ga wadansu mutane wadanda idan da za su addu'a Allah Ya sauko da wannan dutse da ke bayansu to wallahi Allah Zai saukar da shi. Don haka sai suka ja da baya suka ki yin mubahalan, inda suka yi sulhu da Manzon Allah da kuma alkawarin za su dinga aiko da Jizya ga musulmi kowace shekara, don dai a barsu su tafi. Mai Son Karin Bayani Kan Mubahala Yana Iya Matsa Nan.   HAJJIN BAN KWANA   A shekara ta goma bayan hijira, Manzon Allah (s) ya fito, shi da dukkan matansa da ayari mai yawa na daga sahabbansa don yin aikin hajji, hajjin da daga baya ake kira da Hajjin Ban Kwana. Manzon Allah (s) ya isa garin Makka ne a ranar hudu ga watan Zul Hajji. A yayin wannan aikin hajji dai Manzon Allah (s) ya yi jawabi ga dimbin jama'ar musulmi akan Dutsen Arfa, jawabin da har yau din nan yana nan a zukatan musulmi kuma zai ci gaba da zama har tashin kiyama. A yayin wannan jawabi dai Manzo (s) bayan godiya ga Allah Madaukakin Sarki, ya yi cikakken bayani a kan dokoki da ka'idojin Musulunci, sannan kuma ya rushe duk wata al'ada ta lokacin Jahiliyya, ya kuma umarci wadanda ke gurin da su sanar da wadanda ba sa nan. A cikin hudubar tasa ya yi magana a kan mashahurin hadisin nan na Al-Thakalain, wato fadinsa (s) cewa: Allah Ya kira ni, kuma nan ba da dadewa ba zan amsa masa; to amma ni na bar muku wasu nauyaya guda biyu a cikinku: (su ne) Littafin Allah da Zuriyata Ahlulbaiti. Littafin Allah, igiya ce da ke hade daga sama zuwa kasa; Zuriyata kuwa su ne Ahlulbaitina. Lallai Ubangiji Mai Rahama Ya sanar da ni cewa wadannan abubuwa biyu ba za su taba rabuwa da juna ba har lokacin da za su same ni a bakin tafkin Alkausara. Ina mai gargadinku da kar ku kaurace musu. Bayan gama wannan huduba, sai Manzon Allah (s) da tawagarsa suka kama hanyar dawowa Madina tare da dubban sahabbansa da suka rako shi zuwa wannan hajji na ban kwana.  

Tsinkaya Cikin Halayen Manzon Allah (s)

Annabi Muhammadu (s) ya kasance kyakkyawan misali na duk wani cikakken mutum ta kowane bangare. Shi dai ya kasance babban misali na ayyukan kwarai, sannan kuma babban abin koyi ga sauran al'umma. Allah Madaukakin Sarki Ya bambanta shi da sauran mutane ta hanyar tara masa wasu siffofi na cika kamar saukin kai, gaskiya, tausayi, hakuri, biyayya, rikon amana, karfin zuciya, jarumtaka, kyauta, gafara, hikima da dai sauransu. Ta hanyar wadannan kyawawan dabi'u nasa ne ya jagoranci zuriyarsa, sahabbansa, matansa da sauran jama'a. Don haka ya kamata mu yi koyi da darussa masu amfani daga rayuwarsa don mu ma mu aikata su. Al'ummarmu ba za ta taba zama ta Musulunci ba har sai mun bi hanyar wannan Manzon na karshe sau da kafa, mun aikata abin da ya ce, mun kiyaye tsarkakan ayyuka da dabi'unsa, kana kuma mun aikata su kamar yadda muminai daga sahabbansa suka aikata. A takaice, Allah Madaukakin Sarki Ya umarcemu da mu dauki ayyukan Manzo (s) a matsayin abin koyi don kuwa yana shiryar da mu ne zuwa ga kyawawan dabi'u da tsoron Allah. Allah na cewa: Hakika abin koyi kyakkyawa ya kasance a gare ku wajen Manzon Allah, ga wanda ke kaunar Allah da ranar Lahira ya kuma ambaci Allah da yawa. (Surar Ahzab: 33:21) Don haka yanzu ba ri mu yi nazari cikin wasu daga cikin irin wadannan kyawawan halaye na Manzon Allah (s), kamar haka: TUNANI DA HIKIMA Bayan da Manzon Allah (s) ya fito fili da wannan kira nasa da kuma irin karbar da al'umma suka yi wa kiran, sai kafiran Makka suka fara tunanin hanyoyin da za su bi wajen kawo karshen wannan barazana da take fuskantarsu. Don haka sai suka fito wa lamarin ta hanyoyi daban-daban, daga cikin hanyoyin kuwa har takurawa al'ummar musulmin da kuma azabtar da su. sai Manzo (s.a.w.a) ya ga cewa bari ya yi wa wani adadi daga mabiyansa izini da yin hijira zuwa Habasha, don ya samar musu kariya da matsera daga takurawa. Don haka sai mazaje goma sha daya da mata hudu suka yi hijirar, suka saura a Habasha har na tsawon watanni uku, har zuwa lokacin da labari ya isa gare su cewa Kuraishawa sun mika kai. Wannan ya sa suka dawo Makka, sai dai sun sami cewa Kuraishawa na nan da halinsu ba su canza ba, wato dai suna ci gaba da cutar da Musulmi da azabtar da su. Sai Manzo (s.a.w.a) ya hore su da sake yin hijira zuwa Habasha. A wannan karon adadinsu ya kai maza tamanin mata goma karkashin ja-gorancin Ja'afar dan Abi Dalib. Kuraishawa dai sun yi matukar tsorata da wannan hijira, don haka sai suka yi kokarin dawo da su, in ban da cewa sarkin Habasha Najjashi, wanda ke bin addinin Annabi Isa (a.s) a wannan lokacin, ya ki yarda da bukatun 'yan aiken Kuraishawa, wato Amr bin As da Ammara bin Walid. 'Yan aiken na Kuraishawa sun yi kokarin shafa wa musulmin bakin fenti a wajen sarkin Habasha don ya ki karbar masu hijirar; bugu da kari kuma suna dauke da kyautuka masu yawa daga Kuraishawan zuwa gare shi; sai dai kuma jawabin da Ja'afar dan Abi Dalib ya yi a gaban sarkin ya bata musu shiri da kuma sanya sarkin ya ki amincewa da bukatan 'yan aiken, inda ya ke cewa: Ya kai wannan sarki, hakika mun kasance mutanen jahiliyya Muna bautar gumaka, muna cin mushe, muna aikata alfasha, ba ma sadar da zumunci, muna munana makotaka, mai karfi a cikinmu na danne mai rauni. Haka muka kasance har Allah Ya aiko da Manzo zuwa gare mu, wanda mun san danganensa da gaskiyarsa, rikon amanarsa da kamun kan sa; sai ya kira mu zuwa ga Allah don mu kadaita Shi kuma mu bauta mi Shi, mu kuma janye daga abubuwan da muka kasance, mu da iyayenmu, muna bauta musu na daga duwatsu da gumaka. Ya hore mu da fadar gaskiya, rokon amana, sadar da zumunci, kyautata makotaka da kamewa daga da abubuwan da aka haramta da zubar da jinni. Ya kuma hana mu aikata alfasha, shedar zur, cin dukiyar maraya da yin kazafi. Haka ya hore mu da bautar Allah Shi kadai ba tare da mun hada Shi da komai ba. Ya hore mu da yin salla da zakka da azumi. Sai Najjashi ya ce masa: "Ko kana a tare da kai akwai wani abu daga abin da Manzo Muhammadu ya zo da shi daga Allah?". Sai Ja'afar ya ce na'am. Sai ya karanta masa wani sashi na Surar Maryam. Jin wannan aya, sai Najashi da wadanda suke tare da shi na daga malaman Kirista suka fashe da kuka. Sai Najashi ya ce: " Hakika da wannan da abin da Isa ya zo da shi sun fito ne daga tushe guda." Lalacewan shirin Kuraishawa na kawo cikas ga hijira zuwa Habasha ya kara kaimin adawarsu da da'awar Musulunci, don haka sai suka kuduri aniyar lankayawa Bani Hashim takunkumin cinikayya, cudanya da auratayya; sai suka rubuta haka a wata takarda wadda mutane arba'in daga shugabannin Kuraishawa suka rattabawa hannu a kai. Sai suka kange Banu Hashim a Shi'ibi Abi Dalib, suka zama ba sa fita daga wannan guri sai a lokutan Ummura a watan Rajab, da lokacin aikin Haji a watan Zul-hijja saboda girman matsayin a tsakaninsu da sauran Kuraishawa. Musulmi sun shiga wani mawuyacin hali matuka, saboda hatta abincin da zai ishe su ba su da shi, kunci ya kai musu ko'ina. Haka wannan takunkumi ya ci gaba har tsawon shekaru uku, lokacin da takunkumin ya kawo kare yayin da Allah Ya turo sari ya cinye wannan takarda da aka sanyawa hannu, bai bar kome ba sai kalmar Bismikal-Lahumma (wato da SunanKa ya Allah), dake rubuce a saman ta. Wannan al'amari ya yi matukar ruda mushrikai, ya kuma sa musu karin dalili a kan gaskiyar da'awar Manzo (s.a.w.a). SAUKIN KAI DA GIRMAMA MUTANE Duk da cewa takunkumi ya kare, sai dai haka bai zama karshen matsaloli ba; domin Khadija bint Khuwailid, matar Annabi (s.a.w.a) kuma babbar uwar muminai, wadda ta kasance farkon wadda ta bada gaskiya da shi ta kuma gaskata shi, ta kuma yi tarayya da shi cikin wahalhalun isar da sako; ta bayar da dukiyarta saboda Allah. Rasuwarta ta kasance kafin hijira (zuwa Madina) da shekaru uku, kuma a watan Ramalana mai alfarma. Manzo (s.a.w.a) ya ji wannan mutuwa kuma ya yi bakin ciki matuka. Bayan wafatin Khadija (RA) da kwanaki uku kuma sai Abu Dalib, mai kariya ga Annabi kuma madogaran sakonsa, shi ma ya rasu. Labarin rasuwar wannan baffa na shi ya sa shi cikin karin bakin ciki, yayin da ya je wajen gawarsa, ya shafi gefen goshinsa na dama da na hagu, sannan ya ce: Ya baffa, ka reni yaro, ka rike maraya kuma ka yi taimako mai girma, Allah Ya saka maka da alheri a kan abin da ka yi min. Saboda tsananin tasirin wadannan abubuwa biyu a ci-gaban yunkurin tarihin Musulunci ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya sa wa wannan shekara suna Shekarar Bakin Ciki. TAUSAYI DA KYAUTA Saboda kunci da damuwar rashin Matarsa da Baffansa, kana kuma ga sabuwar gaba da kafiran Makka suka dasa saboda karfin gwuiwan da suka samu saboda rasuwar Abu Talib, Manzon Allah (s) ya kuduri aniyar zuwa garin Da'ifa don isar da sakon Musulunci; amma abin takaici mutanen Da'ifan ba su karbi wannan sako ba. Babu wanda ya amsa wannan kira na Manzon Allah (s) in ban da wani tsohon mabiyin addinin Kirista manomi wanda ake kira da Adhasu, shi ne kawai ya karbi Musulunci. Larabawan Da'ifa, maimakon karbar sakon Musulunci, sai suka umarci 'yan iskan gari da kananan yara da su jefi Manzon Allah (s) da duwatsu duk inda ya tafi. Ko da Manzon Allah (s) ya ga wannan sako nasa ba zai yi wani tasiri ga wadannan mutane na Da'ifa masu kekasassun zukata ba, sai ya koma garin haihuwarsa wato Makka. KARFIN ZUCIYA DA JARUMTAKA Bayan dawowa ma dai Manzon Allah (s) ya ci gaba da kiran mutane da kuma kabilu daban-daban zuwa ga Musulunci, sai dai kuma a wannan karon ma dai ba a samu wasu adadi mai yawa da suka karbi wannan da'awa ba. A shekara ta goma sha daya bayan aiko Annabi ne, a lokacin da ya rika bijiro da kiransa a lokutan aikin haji ne ya hadu da wasu mutane daga Khazraj, wadda daya ce daga manyan kabilun nan biyu na Yathrib (wanda ya zama Madina bayan hijira); wadannan mutane ne kuwa suna karkashin jagorancin As'ad bn Zurar, inda ya bijiro musu da Musulunci su kuma suka amsa masa. Wannan tawaga ta yi matukar farin ciki da wannan kira da kuma imanin da suka yi da shi. Daga nan sai wannan shugaba na su ya bukaci Manzon Allah (s) da ya hada su da wani daga cikin sahabbansa don su tafi Yathrib din don ci gaba da isar da sakon Musulunci da kuma karantar da wadanda suka amshi kiran. Hakan kuwa aka yi, sai suka koma Yathrib suna kiran mutane zuwa ga Musulunci. Komawarsu ke da wuya sai suka fara wannan da'awa da kuma kiran jama'a zuwa ga wannan sabon addini kana kuma hanyar tsira duniya da lahira da dukkanin al'umman duniya, amma fa ga wanda ya yi imani da shi. Lalle cikin dan lokaci kadan an samu nasarori kala-kala inda aka samu mutane masu yawan gaske da suka Musulunta. CIKAKKEN MAI GIDA Bayan haka, a shekarar da biyo baya, sai wasu mutum goma sha biyu daga mutanen Yathrib suka je wajen Manzo (s.a.w.a) a Akabah, suka yi mishi mubaya'a a kan cewa: "ba za su hada komai da Allah ba, ba za su yi zina ba, ba za su kashe 'ya'yansu ba, ba za su yi zaluncin da suka kirkira da hannunsu da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba masa a kan wani abu mai kyau ba; in har sun cika alkawarin to suna da Aljanna; in kuwa suka tauye wani abu daga wannan, to al'amarinsu na wajen Allah, in ya so ya azabtar da su, in ya so ya yi musu afuwa." A lokacin aikin hajin da ya biyo bayan wannan, wato a shekara ta goma sha uku da aiko shi, sai wata babbar tawaga daga Yathrib ta yi wani taron asiri da Manzo (s.a.w.a) a Akabah; tawagar ta kunshi maza saba'in da mata biyu. Wannan ne ya samar da wani yanayi da da'awar Musulunci za ta tsayu a kan ta wajen isar da babban sako. Sai Manzo (s.a.w.a) ya hori muminai da yin hijira zuwa Yathrib. Sai Musulmi suka yi ta kwarara, a boye cikin duhu, zuwa gidan imani, suna masu barin dukiyoyinsu da gidajensu saboda addinin Allah Madaukaki.